Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-15 15:34:40    
'Yan wasa na Singapore na begen samun maki mai kyau a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Aminai 'yan Afrika, gasar wasannin Olympics ta Beijing na karatowa. 'Yan wasa na kasar Singapore su ma sun shiga matakin karshe na share fagen halartar wannan gagarumar gasa, wadanda kuma suke begen yin fice a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Kwanan baya ba da dadewa ba, an gudanar da bikin mika tuta ga tawagar wasan motsa jiki ta Singapore dake shirin halartar wasannin Olympics na Beijing. Mista Teo Chee Hean, ministan tsaro kuma shugaban majalisar wasannin Olympics ta Singapore ya yi jawabi a gun bikin, inda ya furta cewa: " 'Yan wasa na Singapore sun riga sun samu ci gaban a-zo-a-gani a gasannin da aka gudanar tsakanin kasa da kasa cikin shekaru goma da suka gabata, wato ke nan sun yi fice sosai a wasannin motsa jiki na Gabashin Asiya, da gasannin wasan motsa jiki na kasashe renon Ingila wato Commonwealth da kuma gasar wasannin motsa jiki ta Asiya da aka gudanar a 'yan shekarun baya, inda suka samu lambobin yabo. Amma babban burin kungiyar Singapore shi ne kwashe lambobin zinariya a gasar wasannin Olympics dake bisa matsayin koli".

An bayyana cewa, a gun gasar wasannin Olympics ta Rome a shekarar 1960, dan wasan daukar nauyi mai suna Tan Hoo Liang na Singapore ya samu lambar azurfa bayan ya lashe sauran abokan karonsa. Amma daga baya, Singapore ba ta taba samun lambobin yabo ba a gun wasannin Olympis da aka gudanar a da. A gun gasar wasannin Olympics da za a gudanar nan gaba kadan a nan Beijing, Singapore ta tsaida kudurin aiko da wata tawagar wasan motsa jiki da ta fi girma tun bayan gasar wasannin Olympics ta Melbourne a shekarar 1956. Wato ke nan 'yan wasa 25 ne na tawagar din ta Singapore za su kara da sauran 'yan wasan kasashen ketare a fannin wasan guje-guje da tsalle-tsalle, da wasan badminton, da wasan kwallon tebur, da wasan iyo, da wasan harbi da kuma wasan tseren kwale-kwale; Ban da wannan kuma 'yan wasa nakasassu na kasar za su shiga gasanni na wasan guje-guje da tsalle-tsalle, da wasan ninkaya da kuma wasan sukuwar dawaki da dai sauransu. Domin samun maki mai kyau a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing a shekarar 2008 da kuma gasar wasannin Olympics ta London a shekarar 2012, tuni yau da shekaru biyu da suka gabata, gwamnatin Singapore ta soma aiwatar da shirin musamman mai lamba " 0812" kan wasannin Olympics da zummar kara inganta aikin horar da 'yan wasa.

Jagoran tawagar Singapore, Tan Eng Liang ya gamsu da ganin yadda 'yan wasan kasarsa suke samun horo yayin da yake cike da kyakkyawan fata ga gasar wasannin Olympics ta Beijing. Yana mai cewa: " Ta kafofin yada labarai ne, muka ga yadda gwamnatin kasar Sin da kuma kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing suke sanya matukar kokari wajen share fagen wannan gagarumar gasa. Lallai muna cike da kyakkyawan fata gare ta. Kuma muna goyon bayar mayar da wasannin Olympics a matsayin wasannin sada zumunta, da taimakon juna, da tabbatar da buri da kuma yin karawa cikin adalci".

Wata 'yan wasa mai suna Toh Li Ying ta Singapore dake shirin halartar wasan tseren kwale-kwale kan teku ta tofa albarkacin bakinta kan halin zuciyarta na shiga gasar wasannin Olympics ta Beijing. Tana mai cewa: " Lallai na yi alfaharin samun damar halartar gasar wasannin Olympics ta Beijing. A yanzu haka dai, muna sanya iyakacin kokari wajen samun horo a kasarmu ta Singapore. Kuma za mu tafi Qingdao na kasar Sin domin samun horo, inda za a gudanar da gasar tseren kwale-kwale kan teku ta wasannin Olympics na Beijing. Mun taba zuwa can don halartar aikin jarrabawa da aka yi, inda akwai kyakkyawan kulob din wasan tseren kwale-kwale da kuma kyawawan otel-otel". (Sani Wang)