Tun can shekaru 2,000 da suka wuce, mutanen garin Jingdezhen sun riga sun fara yin tangaran ta hanyar dakin tuya da aka gina a kan tudu. Amma kafin karni na 10, tangaran da aka fitar daga wannan gari bai yi suna a kasar Sin ba. Tangaran na wannan gari ya kai matsayi na farko ne a zamanin daular Song wato tsakanin shekarar 960 zuwa ta 1279.
A farkon zamanin daular Song, an fi yin tangaran mai launin fari a arewacin kasar Sin, haka nan kuma tangaran da aka fi yinsu a kudancin kasar Sin tangaran ne mai launin shudi. Amma a garin Jingdezhen, an fitar da wani irin tangaran mai launin fari da shudi wanda ba a taba ganin irinsa ba a da.
Bayan da aka kai irin wannan sabon tangaran zuwa fadar sarkin kasar, sai Zhenzong, sarkin kasar Sin a wancan zamanin daular Song ya yi sha'awarsa ainun. Bayan haka Zhenzong, sarkin kasar ya bayar da umurni nan da nan ga garin Jingdezhen don ya yi wa fadar sarkin kasa tangaran, kuma a yi tambarin kirar shekarar Jingde a karkashin tangaran din, sa'an nan ya bayar da umurni don a canja "Changnan" sunan garin nan da ta zama "Jingde".
A albarkacin kulawar da sarkin kasa ke nunawa, tangaran da ake yi a garin Jingdezhen sun sami karbuwa sosai a tarin kasuwannin sayar da tangaran na kasar Sin da sauri, kuma an fara fitar da su zuwa kasar Japan da ta Korea da kasashen kudu maso gabashin Asiya da yankin gabas ta tsakiya da nahiyar Afrika da dai sauran wurare. Ta haka, garin Jingdezhen ya zama wani gari mai arziki, kuma ya zama cibiyar yin tangaran a duk kasar Sin baki daya.
A karshen karni na 13, gwamnatin kasar Sin ta kafa hukumar kula da sana'ar yin tangaran wadda ba a taba kafa irinta ba a cikin tarihin kasar Sin. Kafuwar hukumar nan ta ba da taimako sosai wajen gaggauta yalwata sana'ar yin tangaran a garin Jingdezhen. An fitar da sabbin tangaran iri-iri da aka yi musu kyakkyawan ado. Haka nan ma'aikatan yin tangaran na garin Jingdezhen sun gano wata irin sabuwar kasa mai farin yumbu kuma lallausa kwarai a wani kauye mai suna Gaolin da ke a karkarar wannan gari. Da aka sami irin wannan yumbu, an kyautata ingancin tangaran kwarai, daga nan dai tarihin yin tangaran na Sin da duniya ya sami manyan sauye-sauye. A halin yanzu, yumbun Gaolin ya riga ya zama sunan madaidaicin yumbu da ake yin amfani da shi wajen yin tangaran a duniya.
Tun daga karni na 14 zuwa na 19, an sami bunkasuwa sosai wajen yin tangaran a birnin Jingdezhen. An kafa masana'antu a wannan gari musamman domin yin tangaran da ake samar da su ga fadar sarkin kasar Sin, ta haka garin Jingdezhen ya fara samun wadatuwa kwarai har ba a taba samun irinta ba a da. Sa'an nan an fitar da tangaran na wannan gari zuwa nahiyar Asiya da ta Afrika da Turai da kuma Amurka, har ila yau kuma wasu kasashen Turai ta yamma sun yi odar tangaran daga masana'antun yin tangaran na fadar sarkin kasar Sin a wancan zamani. Haka zalika an fitar da fasahar yin tangaran mai launin shudi da aka yi musu kyakyawan ado zuwa kasar Korea da Japan da Iran da Vietnam da Syria da Masar da kuma Italiya da dai sauran kasashe.
Yayin da ake bunkasa sana'ar yin tangaran a cikin dogon lokaci a birnin Jingdezhen, an fitar da kyawawan tangaran iri dabam daban wadanda aka yi musu ado mai kyaun gani, wadanda kuma ke da daraja kwarai.
|