Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-14 15:23:30    
Burinta na wasannin Olympics ya tabbata

cri

Yara manyan gobe masu yawan gasket a kasar Sin sun sa lura ga wasannin Olympics a kasar Sin.Ga shi a yau za mu gabatar muku da wata karama 'yar jarida mai suna Chen Yanhong wadda ta sa lura sosai kan wasannin Olympics a birnin Beijing,babban birnin kasar Sin, da farko mu ji abin da ta fada a zukatanta. Ta ce" barkanku da wannan lokaci, sunana Chen Yanhong, na z one daga makarantar middle ta ran daya ga watan Augusta ta birnin Beijing. Ina da shekaru 14 da haihuwa, ni yarinya ce mai kishin abubuwa da dama. A halin yanzu wani lokaci na zama mai gabatarwa a cikin shirye-shiryen yara na gidan telibiji na tsakiya, kuma ni yar jarida ce. Ina fatan a gudanar da wasannin Olympics na Beijing na shekara ta 2008 tare da nasara.haka kuma in fatan mutane masu Karin yawa su sa lura kan wasannin Olympics da shiga harkokin wasannin Olympics,haka kuma ina fatan kowa da kowa ya yi kokarin ba da taimakonsa domin maid a duniya da mu ke zama a ciki ta kara kyautatuwa."

Chen Yanhong, yarinya ce mai fasahohi da dama. Da ya ke ita karama ce, tana da kwarewa. A kan matsayin 'yar jarida mafi kuruciya, tare da kwararru 'yan jaridu, ta bayyar da labarai kan yadda aka tafiyar da manyan harkokin siyasa a kasar Sin. Ta taba yin hira da shugaban kasar Sin,ta zama aminiya ta jakadan kasar Amurka a kasar Sin sabo da ta yi hira da shi domin samara da bayanai. A cikin shekaru shida na makarantar firamare, ba ma kawai ta kammala karatunta ba har ma ta sami horo a fannin kida da rawa da sinima, ta fi kwarewa a wasannin raye rare da wake wake, ta taba shiga ayyukan shirya film da wasannin telibiji. Da yak e ta samu ci gaba sosai idan an kwatanta ita da sauran yara masu shekaru daya da ita, Chen Yanhong ba ta nuna girman kai ba. Ubanta Chen Longshi y ace yana fatan diyarta ta samu ci gaba a dukkan fannoni tare da koshin lafiya. Ya bayyana cewa " Mun mai da hankalinmu sosai kan fannoni uku. Na farko muna fatan za ta zama kamila,na biyu muna fatan ta kware wajen yin hulda da jama'a, na uku muna fatan za ta kware wajen aiki. Ta samu irin kwarewa daga zamantakewar jama'a da makaranta da kuma iyali. Idan ba ta iya samu irin ilimi a makaranta ba,mu iyaye mu ba ta ilimin da take bukata a gida. Mun bat a dammar shiga horon samun kwarewa,ciki hard a kos yin koyon raye raye da wake wake da ayyuka na sinima da na talibiji da aikin 'yan jaridu da na masu gabatarwa."

Ga shi a yau dai Chen Yanhong ta kwaru a matsayin 'yan jarida, ta kan yi hira da manyan mutane cikin saki jiki ta yi aikin yadda ya kamata. Amma a karo na farko da ta yi aiki a matsayin 'yar jarida, ta ji tsoro sosai. Ta ce " na ji tsoro kafin in yi hira da baki,zuciyata ta buga kamar ana buga ganga. Da ka zauna ka ga bakon da kake hira da shi ya nuna maka aminci ,sai hankalinka ma ya kwanta.ni yarinya ce,baki sun kan nuna mini kauna,da haka hankalina ya kwanta. Na fi kwarewa wajen yin Magana,na kan ba da misalai da dama,na kan tsara shirin hira na mintoci 15, daga baya hira da na yi da bako ya dau awa sama da daya,sakamakon sha'awarsa ta kara karfi a lokacin hira.na sami nasara wajen yin hira da bako domin samo labarai.

Chen Yanhong ta kara kwarewa bayan da ta yi hira da baki da dama,kullum ta kan mayar da hankalinta kan sabbin al'amuran da suka faru,ta fi mai da hankalinta kan manyan batutuwa na kasa, haka kuma ta mai da hankalinta kan wasannin Olympics a Beijing.kwanakin baya ta yi hira mai ma'ana da Wang ShengAn,kakakin'yan sanada na kungiyar neman dammar shirya wasannin Olympics ta kasar Sin.Chen Yanhong t ace hirar da ta yi da shi ta fadakar da ita kwarai da gasket. Ta ce " Kawu Wang ShengAn ya yi watsi da abubuwa da dama domin kasar Sin ta sami dammar shirya wasannin Olympics tare da nasara,ya fadakar da ni kuma ya burge ni.. na yi hira da shi yayin da yake amsa tambayoyin da na yi masa, ya yi fara'a da farin ciki,ya bayyana nauyin da aka dora masa domin kasa mahaifa da wasannin Olympics. Bayan da aka yi hira, ka ji kamata ya yi za ka bad a taimakonka ga wasannin Olympics.Bayan wannan hira,duk lokacin da ya shiga wasanni ko harkokin da abin ya shafa,ya kan kai ni wurin domin in ganam idona yadda abun ya gudana."

Daga nan Chen Yanhong ta samu Karin damar samo labarai da bayar da su kan wasannin Olympics da harkokin da abin ya shafa. A wannan lokaci, wata dabarar da ta shafi wasannin Olympics ta fado mata, tana so tana gayyatar kwararru 'yan wasan da suka samu lambobin zinariya a wasannin Olympics na Athen na shekara ta 2004 a madadin 'yan makarantun sakandare na kasar Sin. Bayan da ta tattara bayanai da bincike su dalla dalla, ta gano yawansu ya kai 649 wadanda suke cikin kasashe ko nahiyoyi 54 na duniya.sai ta aika takardun gayyata ga jakadu 54 na wadannan kasashe da shugabanni uku na kwamitin wasannin Olympics na duniya. Bisa taimakon da mallamansu da iyayenta suka yi mata, takardun gayyata da ta shirya sun tafi hannanyen jakadun bayan watanni biyu. Chen Yanhong ta karanta abin da ke cikin takardar gayyata. Ta ce" mai martaba jakada;mai martaba shugaban kwamitin wasannin Olympics da wadanda suka samu lambar zinariya; A gabannin wasannin Olympics na Beijing,a matsayina na yar makarantar sakandare mai kishin wasannin Olympics, ina fatan za ku taka muhimmiyar rawa da samu babbar nasara a wasannin Olympics na Beijing,ni kuma 'yar sa kai ce ga wasannin Olympics na Beijing, da zuciya daya ina fatan za ku bayyana abin da ke cikin zukatanku kan wasannin Olympics na Beijing,ku ba mu labarai ko bayanai ko wani abu makamancinsa kan wasannin Olympics,za su zama abu mai daraja da za mu ajiye a cikin dakin nuna kayayyakin tarihi na makarantar sakandare ta ran daya ga watan Augusta ta birnin Beijing.za su karfafa gwiwarmu da mu bi ka'idar wasannin Olympics, bari mu tafi tare a kan hanyar wasannin Olympics da kago sabbin shafuna a cikin wasannin Olympics."

Ga shi a yau dai Chen Yanhong ta sami takardun amsa daga jakadu na Hungary da Jamus da Kenya dake a kasar Sin, ta kuma samu waya daga ofishin jakada na kasar Habasha da na Amurka.Mataimakin shugaban makarantar sakandare ta ran daya ga watan Augusta da Chen Yanhong ke ciki Mr Wang Shidong ya bayyana cewa wadannan takardun amsa sun bayyana fatan alherin jakadun kan wasannin Olympics da samarin kasar Sin,za a tanadi su a cikin dakin nuna kayayyakin tarihi na makarantar sakandare ta ran daya ga watan Augusta.

Yanzu Chen Yanhong tana ci gaba da samu takardun amsa na fatan alheri daga ofisoshin jakadanci na kasashen waje a kasar Sin,burinta zai kara tabbata. Tana so ta zama 'yar jarida a wasannin Olympics na Beijing ta samara da labarai da rahotanni kan wasannin. Muna fatan wannan burinta zai tabbatu.(Ali)