Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-13 18:01:09    
Yawan masu yawon shakatawa a kasar Sin zai karu cikin sauri bayan gasar Olympic

cri

A ran 12 ga wata, Mr. Wang Zhifa, mataimakin shugaban hukumar yawon shakatawa ta kasar Sin ya bayyana cewa, bisa ka'idar da aka saba bi bayan gasannin Olympic na da, sana'ar yawon shakatawa za ta samu bunkasuwa cikin sauri a birnin Beijing da sauran biranen da suke taimakawa gasar wasannin Olympic ta Beijing bayan gasar Olympic ta Beijing. Sabo da haka, hukumomin yawon shakatawa na kasar Sin sun riga sun shirya sosai domin cigaban sana'ar yawon shakatawa bayan gasar Olympic.

"Ya kamata a ce, yawan masu yawon shakatawa da suke kwana a otel-otel da suka kulla kwangila da kwamitin shirya wasannin Olympic ta Beijing ya yi yawa. A tsakanin ran 1 ga watan Agusta zuwa ranar kaddamar da gasar Olympic ta Beijing, yawan masu yawon shakatawa da suka shiga birnin Beijing da sauran biranen da suke daukar wasu gasannin Olympic ya yi ta samun karuwa. Ya zuwa ran 11 ga watan Agusta, yawan kungiyoyin masu yawon shakatawa na ketare da suka je birane 6 da suke gudanar da wasannin Olympic ya kai 175, da ke kunshe da masu yawon shakatawa 6350. A ran 10 ga watan Agusta, yawan dakunan da masu yawon shakatawa suke kwana ya kai kashi 81.2 cikin kashi dari bisa dukkan dakunan otel-otel na wadannan birane. Ya kamata a ce, wannan adadi ya riga ya kai wani matsayi mai kyau."


1 2 3