Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-13 16:49:46    
Wata zakara kuma uwa ta yi ban kwana a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri
A gun gasar wasannin Olympic ta Athens a shekarar 2004, 'yar wasa Xian Dongmei ta kasar Sin ta lashe shahararriyar 'yar wasa Yuki Yokosawa ta kasar Japan a cikin dakika 66 kawai, ta zama zakara, ta haka kasar Sin ta sami lambar zinariya ta farko a cikin gasar wasan judo ta azuzuwan da nauyin 'yan wasa ba shi da yawa. A cikin shekaru 4 bayan gasar wasannin Olympic ta Athens, Xian Dongmei ta yi ritaya, ta kuma haifi wata jaririya, daga baya ta sake kaddamar da aikin horo, a karshe dai ta zama zakara a wajen gasar wasannin Olympic ta Beijing, ta zama zakara kuma uwa ta farko a kasar Sin da ta sami lambar zinariya sau 2 a jere a gun gasar wasannin Olympic. A lokacin da take yin hira da wakilinmu, ko da yake Xian Dongmei ta sha daidaita al'amura da yawa, amma ba ta yi maganganu da yawa ba, sai dai ta nuna kaunarta kan wasan judo da kuma iyalinta. Wakilinmu ya kawo mana wani bayanin musamman kan wannan 'yar wasa ta kasar Sin.

A gun gasar wasannin Olympic ta Athens yau da shekaru 4 da suka wuce, a ganin saura, Xian Dongmei ba ta iya zama zakara ba, amma wannan 'yar wasan kasar Sin ta lashe shahararriyar 'yar wasa Yuki Yokosawa ta kasar Japan a cikin dakika 66 kawai, ta zama zakara, ta haka kasar Sin ta sami lambar zinariya ta farko a cikin gasar wasan judo ta azuzuwan da nauyin 'yan wasa ba shi da yawa. Maganar da ta yi, wato 'ko da yake a ganin saura, ba zan iya samun lambar zinariya ba, amma ni ina nuna aniya a kan kaina', ta shahara, har ma kowa da kowa ya tuna da ita. Bayan gasar, wannan tsohuwar 'yar wasa ta kusantar da kanta daga filin wasa, ta kuma haifi wata jaririya a shekarar bara.

Shiga gasar wasannin Olympic da aka shirya a nan Beijing na da muhimmiyar ma'ana. Saboda malamin horas da wasanni da kuma iyalinta sun karfafa gwiwarta, Xian Dongmei ta yanke shawarar sake shiga gasanni. Don haka, ta bar diyyarta mai watanni 4 kawai da haihuwa, ta kaddamar da aikin horo.

Ko da yake Xian Dongmei ta kan nuna gwarin gwiwa a cikin gasa, amma ta nuna kaunarta ga diyarta a lokacin da take hira da wakilinmu bayan gasar. Tana son ta ba wannan lambar zinariya ga diyata a matsayin abin kyauta. Ta ce,'Zan koma gida ba tare da bata lokaci ba, zan iya saduwa da ita cikin sauri. Na dade ina yin aikin horo, ban iya kulawa da ita da kaina ba. Shi ya sa zan raka ta, zan kara kula da ita.'

Bayan da Xian Dongmei ta sake gudanar da aikin horo, ta maido da karfinta cikin sauri. A wajen gasar fid da gwani ta wasan judo ta kasa da kasa a tsakanin kungiyoyi da aka yi a karshen shekarar bara, Xian Dongmei ta shiga shirye-shirye 2, ta taimaka wa kasar Sin da ta zama farko. Sa'an nan kuma, ta sami lambobin zinariya 2 a cikin gasanni 2 na matsayin koli na Turai a wannan shekara, a karshe dai, Xian Dongmei ta sami damar shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Ba za a iya gane wahalhalun da Xian Dongmei ta sha a kan hanyar neman samun nasarar sake bullowa a gun gasar wasannin Olympic ba, sai ita kanta da kuma Fu Guoyi, malaminta na horas da wasanni su ne kawai. Babu mamaki Mr. Fu ya ji farin ciki sosai har ma ya sa Xian Dongmei a kafadarsa bayan gasar. A lokacin da yake zantawa da 'yan jaridu, idanun Mr. Fu cike suke da hawaye, ya yi bayani kan wahalar da suka sha a kan hanyar neman samun wannan lambar zinariya. Ya ce,'A cikin wannan shiri, wato wasan judo na ajin da nauyin 'yan wasa bai kai kilo 52 ba, wasu 'yan wasa sun sake gudanar da aikin horo domin cika burinsu, sun kuma yi kokari sosai, amma ba su iya cika burinsu ba. Yau Xian Dongmei ta zama ta farko a cikin rukunin wasan judo, wadda ta sake gudanar da aikin horo, ta kuma sake samun lambar zinariya a wannan shiri, ta yi fintikau sosai.'

A tarihin wasannin motsa jiki na kasar Sin, ba safai a kan samu 'yan wasan da suka sake gudanar da aikin horo domin shiga gasar wasannin Olympic bayan da suka yi ritaya, kuma suka ji haihuwa, balle ma 'yan wasan judo da su kan fuskanci takara mai zafi. Xian Dongmei ta bayyana cewa, dalilin da ya sa ta tsai da kudurin sake gudanar da aikin horo domin shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing, shi ne domin gwada karfinta, ko za ta iya ko kuma ba za ta iya ba. A kasashen ketare, 'yan wasa da yawa sun shiga gasannin duniya tare da iyalansu, amma galibin 'yan wasan kasar Sin su kan yi ritaya bayan da suka yi haihuwa. A tsakanin dukkan 'yan wasan judo na kasar Sin, ita ce kawai da ta ci gaba da aikin horo bayan da ta haihu.

Ko da yake Xian Dongmei ta riga ta haihu, amma duk da haka, karfinta bai raunana ba a cikin gasa, ta nuna gwaninta sosai kamar yadda ta kan nuna a da. Tsaron kanta yadda ya kamata da kuma kai hari cikin sauri sun taimaka wa Xian Dongmei da ta lashe 'yar wasa daga kasar Korea ta Arewa a cikin karon karshe na shirin wasan judo na ajin da nauyin 'yan wasa bai kai kilo 52 ba a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing, ta sake samun lambar zinariya a cikin wannan shiri. Ba tare da buya kome ba, bayan gasar Xian Dongmei ta gaya mana cewa, ba ta ji babban bambanci sosai ba, in an kwatanta yau da shekarar 2004, sai dai tana begen diyarta. Ta ce,'Babu bambanci a gare ni. Ko da yake saboda shekaruna da haihuwa ya karu kadan, shi ya sa mai yiwuwa ne ba zan iya maido da karfi cikin sauri bayan aikin horo ba, amma burina da kuma aniyata ta shiga gasar wasannin Olympic duk daya ne bisa na da. Ko shakka babu watakila akwai dan bambanci, wato a lokacin da nake gudanar da aikin horo na yau da kullum, na kan yi begen diyata.'

Xian Dongmei ba ta nemi kara yin suna ko kuma samun karin dukiyoyi ba, sai kaunar da take nunawa kan wasan judo ta sanya wannan 'yar wasan kasar Sin ba ta nisantar da kanta daga filin wasa ba. Ko yin ritaya ko kuma sake gudanar da aikin horo domin shiga gasar wasannin Olympic, Xian Dongmei ba ta rasa goyon baya daga iyali da kuma abokai ba. A lokacin da take waiwaya abubuwan da suka faru a da, Xian Dongmei ta fi son bayyana cewa,'Ina son in nuna wa mutanen da suke mara mini baya da kuma iyali da abokai godiya, na gode musu sosai bisa goyon baya da karfafa gwiwar da suka dade suke nuna mini.'

A da Xian Dongmei ta taba bayyana sau da yawa cewa, in ba a yi gasar wasannin Olympic ta karo na 29 a Beijing ba, to, tabbas ne ba za ta sake gudanar da aikin horo ba. Tabbas ne za a sha wahalhalu a kan hanyar sake gudanar da aikin horo, haka kuma za a gamu da matsaloli da yawa a kan hanyar sake samun lambar zinariya. Bayan da ta sake samun nasarar kalubalantar kanta, Xian Dongmei ta kusan cika dukkan burinta a ranta na wasannin Olympic. Mai yiwuwa ne za ta yi hutu, za ta ji dadin zamanta tare da diyarta da kuma iyalinta. Xian Dongmei ta ce,'Yanzu a ganina, ina bukatar hutu mai kyau. Aikin horo da gasanni sun yi zafi sosai, yanzu hutu ya fi muhimmanci a gare ni.'

Wasan judo ya iya kyautata fasahar mutum da kuma zuciyar mutum duka. Samun lambar zinariya na da muhimmanci sosai, amma a gaskiya ko zama zakara ko kuma a'a, a idon Xian Dongmei, mai shekaru 33 da haihuwa ta iya yin ban kwana yadda ya kamata a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing.(Tasallah)