Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-13 15:10:34    
Shirya wasannin Olympics zai ba da taimako wajen daga kwarjinin birane

cri

Birnin Paris, babban birnin kasar Faransa gari ne na Pierre de Coubertin, mahaifin wasannin Olympics na zamani. Bisa rawar da ya taka, birnin Paris ya shirya wasannin Olympics na lokacin zafi har sau biyu, wato a shekara ta 1900 da shekara ta 1924. Ko da yake wasannin Olympics na wadannan karo biyu sun riga sun wuce, amma ba za a manta da alheri da suka kawo wa birnin Paris a fannin sha'anin yawon shakatawa ba. To yanzu ga cikakken bayani.

Paul Roll shi ne shugaban hukumar yawon shakatawa ta birnin Paris. Yana ganin cewa, albarkatun yawon shakatawa wani tushe ne wajen raya sha'anin yawon shakatawa na wani birni ko wata kasa. Kuma shirya gagaruman wasannin motsa jiki musamman ma shirya wasannin Olympics hanya ce mafi kyau wajen karfafa kwarjini na wani birni har ma wata kasa. Kuma ya kara da cewa,

"Dukkan gagaruman wasannin motsa jiki za su samar da wata kyakkyawar dama ga biranen da suka dauki nauyin gudanarwa wajen nuna kansu. Tare da ingantuwar burin kasashe daban daban na kara tuntuba da kuma fahimtar juna, biranen suna iya nuna kyan ganinsu a fannoni daban daban ba fannin wasannin motsa jiki kawai ba ta hanyar shirya manyan wasannin motsa jiki."

Yanzu ana ta samun dimbin hanyoyi wajen watsa labarai, har ma ana iya sanin wasu kananan garuruwa na kasashen waje bisa karfin kafofin watsa labarai. Sabo da haka, ko shakka babu biranen da suka dauki nauyin gudanar da wasannin Olympics za su zama manyan taurari da ke jawo hankulan mutane sosai bisa labarai masu dimbin yawa da kafofin watsa labarai na duk duniya suka bayar a kansu. Kuma Mr. Roll ya bayyana cewa,

"Gagaruman gasanni na duniya za su taka muhimmiyar rawa wajen kara kyautata sifar wani birnin ko wata kasa gaba daya. A duniyar yau, kowa yana iya zuwa kasashen waje da kuma sayen kayayyakin kasashen waje. Sabo da haka ko shakka babu iznin shirya gasar wasannin Olympics da ta kan jawo hakalin duniya zai zama wani abu mai daraja sosai."

Ban da gasar wasannin Olympics ita kanta, Mr. Roll yana ganin cewa, ayyukan share fagen gasar su ma za su sa kaimi wajen kyautata sifofin birane masu daukar nauyin gudanarwa. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da gasar wasannin Olympics ta kan bukaci a raya birnin da zai dauki nauyin gudanar da ita daga dukkan fannoni, da kuma tsara shirin samun bunkasuwa cikin wani lokaci, hakan zai gaggauta bunkasuwar birnin. Kuma Mr. Roll ya ce,

"Gasar wasannin Olympics na sa kaimi ga kyautata ayyukan ba da hidima na birnin da ke daukar nauyin gudanarwa, kamar kara raya muhimman ayyukan yau da kullum da kuma filaye da dakunan wasanni. Da yake a kan tsara takamaiman lokacin bude gasar wasannin Olympics, shi ya sa dole ne a kammala dukkan ayyukan share fage kafin lokacin, ta haka an kara saurin bunkasuwar birnin in an kwatanta da lokacin babu shirya gasar."

A karshe dai Mr. Roll ya bayyana fatan alheri da ya yi wa gasar wasannin Olympics ta Beijing. Ya ce,

"Shirya gasar wasannin Olympics wata kyakkyawar dama ce, inda kasar Sin take iya nuna wa mutanen duniya birnin Beijing da al'adun kasar Sin da ba su fahimta sosai ba, ta yadda za su iya more irin wannan al'adun gargajiya na musamman na kasar Sin. Na yi imanin cewa, tabbas ne kasar Sin za ta yi amfani da damar wajen kammala wannan aiki."(Kande Gao)