A cikin 'yan shekarun baya, batun maganin sa kuzari yana ta damun wasannin motsa jiki. Sau da dama ne, shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa, Jacques Rogge ya bayyana cewa, bisa ka'idar "rashin sassauci ko kadan", za a kara karfin yaki da maganin sa kuzari a gun wasannin Olympics na Beijing.
Matsalar maganin sa kuzari ta fito ne a karshen karni na 19, kuma a shekarun 1960, ta fara jawo hankulan gamayyar kasa da kasa da na 'yan wasa. Sabo da haka, a gun wasannin Olympics na Mexico da aka yi a shekarar 1968, a karo na farko ne aka fara gudanar da binciken maganin sa kuzari a kan 'yan wasa na kasashe daban daban. Yau shekaru 40 sun wuce, amma ana ci gaba da fuskantar babban kalubale a fannin yaki da shan maganin sa kuzari. Sabo da haka, kara karfin binciken maganin sa kuzari ya zama bukata ta kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa, da kuma niyya ta kasar Sin, haka kuma buri daya na duk duniya."Muna kokari domin wasannin Olympics da ke da muhalli mai kyau da kuma rashin samun shan maganin sa kuzari. Ina kin jinin maganin sa kuzari. Na farko, ya lalata lamunin na wasannin motsa jiki. Wasanni na girmama sakamakon da 'yan wasa suka samu, amma idan an sami sakamakon ne ba bisa kokarin da aka yi ba, lallai, ko kadan ba shi da daraja. Na biyu kuma, maganin sa kuzari na da hadari sosai ga lafiyar 'yan wasa, sabo da haka, tilas ne mu kare 'yan wasa."
A game da matakan da aka dauka a gun wasannin Olympics na Beijing a fannin binciken maganin sa kuzari, shugaban sashen likitanci da kimiyya na kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa, Dr.Patrick Schamasch ya ce, "A gun wasannin Olympics na Beijing, za a gudanar da binciken maganin sa kuzari har sau 4500 a wajen gasanni ko waje da gasanni, wanda ya fi yawa a tarihin wasannin Olympics. Adadin ya karu da kashi 25% bisa na wasannin Olympics na Athens a shekarar 2004 da kuma kashi 90% bisa na wasannin Olympics na Sydney a shekarar 2000."
Ban da wannan kuma, a gun wasannin Olympics na Beijing, za a fi ladabtar da 'yan wasan da aka gano suna amfani da maganin sa kuzari. Wato ban da aiwatar da ka'idojin hukunci na kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa da kuma na kungiyoyin wasanni iri iri, za a haramta 'yan wasan da aka yanke musu hukuncin daina shiga wasanni cikin watanni shida ko fiye, zuwa wasannin Olympics na London na shekarar 2012. Sa'an nan, za a rike samfurorin bincike har cikin tsawon shekaru 8, wato mai yiwuwa ne za a sake yi musu bincike.
Bayan haka, an kuma yi amfani da wasu sabbin fasahohi a wajen binciken maganin sa kuzari. A asibitin Xiehe da ke birnin Beijing, an kafa dakin binciken jinsin 'yan wasa na farko a tarihin wasannin Olympics, inda za a bincike 'yan wasan da ake shakkarsu.
Ka'idar "rashin sassauci ko kadan" kan maganin sa kuzari ya sami goyon baya daga dimbin 'yan wasa. A gun bikin fara wasannin Olympics na Beijing, a madadin dukan 'yan wasa ne, 'yar wasa ta kasar Sin, Zhang Yining ta yi rantsuwa cewa, "Da sunan dukan 'yan wasa ne nake cewa, domin alfarmar wasanni da ta tawagogi, za mu shiga wasannin Olympics a wannan karo bisa da'ar wasanni, kuma nuna biyayya ga ka'idoji daban daban na wasanni, don tabbatar da rashin samun maganin sa kuzari a gun wasannin."
Yaki da maganin sa kuzari da kiyaye kwarjinin wasannin Olympics da tabbatar da tsabta da adalci a gun wasannin Olympics, buri ne na kasashe daban daban ga wasannin Olympics na Beijing, haka kuma alkawari ne da Sin ta dauka ga duniya.Yanzu gasanni na gudana kamar yadda aka shirya. Da sahihin zuci ne ake fatan lambobin yabo da 'yan wasa za su samu za su bayyana ainihin karfinsu.(Lubabatu)
|