A ranar 11 ga wannan wata a nan birnin Bejjing, kakakin hukumar motsa jiki ta birnin Beijing mai suna Sun Xuecai ya bayyana cewa, a cikin shekaru biyar da suka wuce, birnin Beijing ya yi amfani da dama mai kyau ta shirya wasannin Olimpic wajen bunkasa sha'anin kara lafiyar jama'a, himmar da mazauna birnin Beijing suka yi don shiga ayyukan motsa jiki ta kara daguwa fiye da kima. Sakamakon da aka samu bayan bincike ya bayyana cewa, kashi 85 cikin dari na yawan mazauna birnin Beijing sun riga sun kai matsayin da kasar Sin ta tsai da wajen binciken ingancin lafiyarsu, kuma ingancin lafiyarsu ya kara karuwa.
A gun taron manema labaru da aka shriya a wannan rana, Mr Sun Xuecai ya bayyana cewa, ya zuwa karshen shekarar da ta shige, an kafa kayayyakin motsa jiki na kara lafiyar jama'a a dukkan titunan birnin da kauyuka da garuruwa na Beijing. Sa'anan kuma, don biyan bukatun da bambancin mutane suka yi wajen kara lafiyarsu, birnin Beijing ya kuma zuba kudaden da yawansu ya kai kudin Sin Yuan miliyan goma, ya kuma gina rumfunan nuna wasan kwallon tebur da filayen nuna wasan kwallon kwando fiye da 60 a unguwoyi daban daban na birnin don samar da damar yin wasan kwallo iri iri ga yara bayan ajinsu. Mr Sun Xuecai ya bayyana cewa, a cikin shekaru biyar da suka wuce, yawan mutanen da suka shiga ayyukan motsa jiki don kara lafiyarsu ya kara karuwa, ingancin lafiyarsu ya kara daguwa a bayyane, hakan kuma tunaninsu na yin ayyukan mota jiki don kara lafiyar ya kara karfafa sosai. A shekarar bara, a duk birnin Beijing, an shirya gasar wasannin kwallon tebur a tsakanin unguwoyi daban daban, da akwai tituna 314 tare da unguwoyi 2523 da kauyuka 3974 da suka yin rajistar shiga gasar, wannan ne gasar da aka shiga tare da mutane mafi yawa a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce.
Yanzu, a birnin Bejing, ana kan shirya bikin yin dogwayen guje-guje na kasa da kasa na birnin Bejing da gasar wasan badminton da mutane dubu suka shiga a ciki da gasar wasan kwallon kwando don cin kofin shimfida unguwoyi masu jituwa da sauransu, wato gassani 15 ke nan, sa'anan kuma ya riga ya kafa tashoshi kusan dubu 5 na ba da taimako ga wadanda suke yin wasan motsa jiki a safiya da maraice na kowace rana. Ban da wannan kuma, a birnin Beijing, an kuma sami lambunan shan iska 11 da ke da halayen musamman wajen yin wasan motsa jiki.
A sa'I daya kuma, birnin Beijing ya yi kokarin raya hadaddun kungiyoyin wasannin motsa jiki , gwamnati kuma ta yi musu shugabanci a manyan fannoni, kuma kungiyoyin wasannin motsa jiki masu yawa sun ba da taimako ga shirya gasannin wasanni. Yanzu, birnin Beijing ya sami hadaddun kungiyoyin wasannin motsa jiki da yawansu ya kai 77, dukkan tituna da unguwoyi da kauyuka da garuruwa na birnin sun kafa kungiyoyin wasannin motsa jiki. Mr Sun Xuecai ya bayyana cewa, yanzu, birnin Beijing tana nan tana sa kaimi ga gudanar da wasannin motsa jiki bisa tsarin haduwar kungiyoyin wasannin motsa jiki da zamantakewa al'umma, wasu kungiyoyin wasannin motsa jiki su da kansu su shirya gasannin wasannin motsa jiki, alal misal, hadadiyyar kungiyar wasan kwallon kwando ita da kanta ta shirya wasu gasannin wasan kwallon kwando a tsakanin sinawan da ke zama a gida da waje.
Mr Sun Xuecai ya bayyana cewa, 'yan wasa masu asalin birnin Beijing da yawansu ya kai 44 sun shiga kungiyar wakilan kasar Sin da ke halartar wasannin Olimpic na Beijing, daga cikinsu da akwai Zhang Yining da He Kexin da Lin Yue da sauransu. (Halima)
|