Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-12 15:16:17    
An nuna yabo sosai ga abincin musulmi na kauyen 'yan wasannin Olympics

cri

Domin samar da abinci mai inganci da kuma dadin ci har na tsawon sa'o'i 24 a ko wace rana, a kan sha aiki sosai a cikin babban dakin cin abinci da fadinsa ya kai kusan murabba'in mita dubu 20 a cikin kauyen 'yan wasannin Olympics na Beijing. Haka kuma domin biyan bukatun 'yan wasa na kasashe daban daban wajen abinci, dakin cin abinci ya samar da abincin Judah da na musulmi da na Indiya da dai sauransu, a ciki, abincin musulmi ya samu yabo sosai daga wajen baki musulmai. To yanzu ga cikakken bayani.

Lokacin da Mohammed Ghamin, shugaban kungiyar 'yan dambe ta kasar Masar ke zantawa da wakilinmu, ya bayyana ra'ayinsa kan kayayyaki da kuma ayyukan ba da hidima na kauyen 'yan wasannin Olympics. Kuma ya ce, kauyen yana da tsabta, kuma ana iya samun kayayyaki iri daban daban da ake butaka da kuma kyawawan ayyukan ba da hidima, shi ya sa suka kasance tamkar sarakuna a cikin kauyen. Ban da wannan kuma Mr. Ghamin ya yaba wa dakin cin abinci da kuma abinci na kauyen, ya ce,

"Dakin cin abinci na kauyen 'yan wasannin Olympics ya yi kyau sosai, har ma ya wuce abin da kake tsammani a zuciya, ana iya samun abinci iri daban daban, kamar Pizza da burodi da nama da kifi da kuma 'ya'yan itatuwa iri iri da Salad da abin sha da dai sauransu. A gaskiya dai, in ba ka tsara shiri kan abin da kake so kafin ka je dakin cin abinci ba, to tabbas ne za ka rude a gaban wadannan dimbin ire-iren abinci. A galibi dai, wannan dakin cin abinci yana da aji na farko, kuma yana iya biyan bukatun dukkan 'yan wasa."

Mr. Ghamin ya taba shugabantar 'yan dambe na kasar Masar wajen shiga wasannin Olympics na Atlanta da na Sydney da kuma na Athens. A matsayinsa na shugaban kungiyar musulmai da ya zo daga wata kasar Larabawa, Ghamin yana mai da hankali sosai kan abincin musulmi na kauyen 'yan wasannin Olympics. Kuma ya gaya mana cewa,

"Ma'aikata na dakin cin abinci sun shatta wani layi domin raba abincin musulmi da sauran abinci, sabo da haka 'yan wasa musulmai suke iya kwantar da hankulansu wajen cin abinci. Ban da wannan kuma idan 'yan wasa musulmai sun nuna sha'awa ga wani irin abinci da ke waje da layin, to za su sanin ko wannan abincin musulmi ne ko a'a, matukar sun tambayi masu ba da hidima da ke kusa da su."

Bayan da wakilinmu ya yi intabiyu tare da shugaban kungiyar 'yan dambe ta kasar Masar, ya gamu da Aberra Aguegnehu, mai aikin fassara na kwamitin wasannin Olympics na duniya a cikin kauyen 'yan wasannin Olympics. Mr. Auegnehu, wani dan kasar Habasha ne da aka haife shi a kasar Pakistan. Ko da yake yana bin addinin Kirista, amma har kullum yana zama tare da musulmai tun yarantakarsa. Sabo da haka, yana iya sabawa da abincin musulmi da ba na musulmi ba. A matsayinsa na zaunannen mai aikin fassara na shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya, wannan shi ne karo na 7 gare shi wajen sa hannu a cikin ayyukan fassara na wasannin Olympics a jere. Lokacin da yake tabo magana kan dakin cin abinci na kauyen 'yan wasannin Olympics, Mr. Aguegnehu ya bayyana cewa,

"Yau abin da na ci shi ne abincin musulmi, dakin cin abinci na kauyen 'yan wasannin Olympics ya ba mu mamaki sosai, kuma shi ne dakin cin abinci mafi kyau da na taba gani."(Kande Gao)