Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-10 21:39:18    
An shiga kwana na biyu da gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Guo Jingjing da Wu Minxia

Yau ranar 10 ga wata, an shiga kwana na biyu da gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing, ya zuwa karfe 5 da mintoci 40 na yamma, gaba daya aka samu lambobin zinariya guda 9 na manyan ayyukan wasa hudu na wasannin iyo da harbe-harbe, da kada tsalla cikin ruwa, da kuma daukar nauyi.

A ranar 10 ga wata da safe, 'dan wasan iyo na kasar Amurka Michael Phelps ya karya matsayin bajimta na duniya kuma ya samu lambar zinariya a gasar iyo mai salo daban-daban na mita 400 na maza.

Haka kuma 'dan wasan iyo na kasar Korea ta kudu Park Taehwan ya samu lambar zinariya da mintoci 3 da dakika 41.86 a gun gasar iyo cikin 'yanci na mita 400 na maza. 'Dan wasan iyo na kasar Sin Zhang Lin ya samu lambar azurfa a gasar, wadda ta zama lamba ta farko da 'yan wasa maza na kasar Sin suka samu a gun gasannin iyo na wasannin Olympics.

A gun gasar mai salo daban-daban na mita 400 na mata, 'yar wasa ta kasar Australiya Stephanie Rice ta karya matsayin bajimta na duniya kuma ta samu lambar zinariya da mintoci 4 da dakika 29.45.

A gun gasar iyo cikin 'yanci na yada kanin wani na tsawon mita dari-dari na mata hudu-hudu, kungiyar kasar Holland ta samu lambar zinariya da mintoci 3 da dakika 33.76 a yau da safe.

A gasar harbe-harben fistole na mita 10 na mata, 'yar wasa ta kasar Sin Guo Wenjun ta samu lambar zinariya da zobba 492.3.

A cikin gasar taka tsalle cikin ruwa mai katako na tsayin mita uku na mata, 'yan wasa na kasar Sin Guo Jingjing da Wu Minxia sun samu lambar zinariya.

A gun gasar harbe harben bindiga daga fannoni daban-daban na maza, 'dan wasa na kasar Czech Kostelecky David ya samu lambar zinariya.

A gun gasar daukan nauyi na ajin kilo 53, 'yar wasa ta kasar Thailand P. Jaroenrattanatarakoon ta samu lambar zinariya. A gun tseren keke kan hanyar mota ta mata, 'yar kasar Ingila Nicole Cooke ta samu lambar zinariya.(Danladi)