Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-09 00:22:09    
Sakonnin masu sauraro a kan wasannin Olympics na Beijing

cri

Yau ne aka bude wasannin Olympics a nan birnin Beijing, kuma yanzu duk duniya na zura ido ga birnin Beijing da kuma kasar Sin. Masu sauraronmu ma suna sa rai sosai a kan wasannin Olympics na Beijing, kuma kwanan nan, sun rubuto mana sakonni da yawa, don nuna goyon baya da fatan alheri ga wasannin Olympics na Beijing.

Mamane Ada, wanda ya zo daga birnin Yamai, jamhuriyar Nijer, ya rubuto mana cewa, "kamar yadda hankalin kasashen duniya ya karkata zuwa kasar Sin, to haka ne su ma 'yan Nijar suke alfahari da wannan wasanni na kasa da kasa. Ganin cewa kasar Nijar za ta halarci wannan konbala a fannoni daban daban ne, ya sa al'umar Nijar take fatan kasar Sin za ta cimma burinta wajen shirya wannan wasanni cikin lumana da jin dadin kowa. Masu sauraren cri dake nan birnin Yamai muna kira da cewa, a lokacin wannan wasanni, ku rika bada labaru kan 'yan wasan Nijar dake cikin wannan konbala."

To, madallah, Mamane Ada, muna maka godiya da rubuto mana wannan wasika, ba shakka, a lokacin wasannin Olympics, za mu mai da hankali sosai a kan 'yan wasan kasashen Afirka, ciki har da Nijer, kuma za mu dinga ba da labarai a kansu, da fatan za ku kasance tare da mu a kullum, don ku dinga samun labaran 'yan wasan Nijer. Bayan haka, muna kuma fatan 'yan wasan Nijer za su cimma burinsu a gun wasannin Olympics na Beijing.

Sa'an nan, Mohammed Idi Gargaji?a, shugaban kungiyar masu sauraron CRI da ke jihar Gombe, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa,

"A matsayinmu na abokan jama'ar kasar Sin baki daya, ko shakka babu muna jin murna da farin ciki kwarai da gaske game da gasar wasannin olympic ta Beijing 2008. Sabo da haka, yanzu dukkan hankulanmu sun karkata ne kacokam kan birnin Beijing. Lallai ba shakka a ganinmu birnin Beijing ya cika dukkan alkawuran da ya dauka na shirya gasar wasannin olympic Beijing 2008.

Ban da wannan kuma, abin farin ciki shi ne birnin Beijing ya kara tsaftacewa da mutuntawa da kuma darajanta wasannin olympic ta dukkan fannoni daban daban, ba ga yan wasa kawai ba, harma ga dukkan al'ummar duniya baki daya.

Daga karshe muna fatan Beijing zai samu cikakkiyar nasara wajen gudanar da wannan gaggarumin biki mafi ban sha'awa da ban mamaki da kuma ban al-ajabi, sa'annan kasar Sin tana da nasara kuma za ta yi nasara a gun gasar wasannin olympic ta Beijing 2008 wajen samun lambobin yabo na zinariya mai daraja."

Sa'an nan, Salisu Dawanau daga Garki Abuja, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, "Duniya za ta ga bukukuwa da kade-kade da raye-raye da kuma wasanni daban-daban a ranar da za'a bude gasar wasannin Olympic na Beijing. Ni da sauran aminai da abokan kasar Sin, a ranar 8 ga Agusta, cike muke da farin ciki. Muna fata za a fara gasar Olympic din cikin nasara da kuma kammalawa gasar cikin nasara.

Hankalinmu da tunaninmu zai koma Beijing daga ranar 8 din don gane wa idanunmu abubuwan da za'a yi wasannin a kai."

Bayan haka, Bala Muhammed Mando daga Abuja, Nijeriya, ya rubuto mana cewa, "ina matukar farin cikin ganin yadda kasar Sin ta yi gagarumin shirin wannan wasanni na Olympics 2008, kuma ba na shakka ko kadan cewa za a samu muhimman nasarori masu yawa domin kasar Sin ta shahara sosai a fannoni daban daban a duniyar nan. A kullum ina kidaya kwanaki har zuwa 8 August, kuma zan kasance a gaban akwatain talabijin dina daga farko har zuwa karshen wasannin. Ina ma dukkan jama'ar Kasar Sin da gwamnatin Kasar da kuma Gidan Rediyon CRI addu'ar farawa da kuma kammala wannan gasar olympic lafiya. Amin."

To, sai kuma Musa Abubakar Adamu, shugaban kungiyar masu sauraronmu ta jeka da fari, ya rubuto mana cewa, "ganin yadda kuke watsa shirye-shirye a kan wasan Olympic na Beijing da karfin gwiwa ya sa ni da wasu sassa na membobina muka shirya wadannan baitoti:

Yaku jama'a mu koma kasar Sin#

Domin itace uwa ba da mama.

Duk wanda yake son kasar Sin#

Lallai yana da tunani mai hikima.

HU JIN TAO na kasar Sin#

Yana kokarin ci gaban al'umma.

Ku sani Olympic na kasar Sin#

Zai ba da babbar nasara ga al'umma.

Yau kowa na bukatar kasar Sin#

Domin itace kasa ba da mama.

Uwar kasa itace kasar Sin#

Domin lura da damuwar al'umma.

Al'umma suna walwala a kasar Sin#

Domin wasan olympic na al'umma.

Bana za'a kara a kasar Sin#

Wajen wasan olympic na al'umma.

Kakar bana na olympic na kasar Sin#

Zai tara abubuwa da yawa har da al'umma.

Ku sani kasa mai girma itace kasar Sin#

Wajen biyan bukatun al'umma.

Wajen kula da baki a kasar Sin#

Mutane kamar suna wajen al'umma.

Beijing olympic 2008 na kasar Sin#

Zai hada kan dukkan al'umma.

Wasan olympic na bana a kasar Sin#

Zai bar muhimmin tarihi ga al'umma.

Sauran kasashe kuyi koyi da kasar Sin#

Domin samun darasin gaskiya ga al'umma.

Mu mun yi imani cewa kasar Sin#

Ita ce uwa ba da mama ga al'umma.

CRI 'yar kwarai ta kasar Sin#

Tana kokari don wayar da al'umma.

Wasan olympic na kasar Sin#

Kai ka ce CRI ce zata yiwa al'umma.

Domin bayyana shi ko da yaushe a kasar Sin#

Har da duniya gaba daya ga al'umma.

A gaishe ki CRI na kasar Sin#

Bisa gagarumin aiki domin al'umma.

Ku gaishe da HU JIN TAO na kasar Sin#

Da duk mataimakansa na kwarai daga al'umma.

Domin suna son cigaban kasar Sin#

Tare da dawainiyar dukkan al'umma.

JEYRALA na fatan alheri ga kasar sin#"

To, a gaskiya 'yan baitocin sun burge mu sosai da sosai, kuma muna yi wa dukan mambobin kungiyar Jeyrala godiya, sabo da goyon bayan da kuka ba mu, mun gode. Allah ya saka da alheri.

Bayan wannan, wasu masu sauraro sun kuma rubuto mana shawarwarinsu dangane da shirye-shiryenmu a lokacin wasannin Olympics. Kamar yadda ya rubuta a cikin wasikarsa, Idris Dagalan ya ce, "Game da gasar Olympic ta bana, na fi son samun bayanai akan wasan gudu na mata da maza,wasan kwallon kafa,wasan laun-tainis da kuma wasan kwallon kwando."

Sa'an nan, malami Yusuf ya rubuto mana cewa, "Madallah da matsowar wannan gasar.wasannin da kowa yake da burin yaji bai wuce wasanni da duk Duniya ta raja'a a kai ba, wato kwallon kafa. Zai yiwu jama'a su dinga son su ji tarihin 'yan wasan.cikin bayanin ko wane wasanni da yake cikin afkuwa a wannan lokacin."

To, mun gode muku da ba mu shawarwarin, kuma za mu yi kokarin biyan bukatunku, muma kuma fatan za ku dinga kasancewa tare da sashen Hausa na rediyon kasar Sin a lokacin wasannin Olympics.

Masu sauraro, "duniya daya, mafarki daya". An fara wasannin Olympics a nan birnin Beijing, kuma 'yan wasa da jama'a sun taru a nan birnin Beijing domin wasannin Olympics, domin mafarkinsu daya na Olympics. Beijing a shirye take, kuma tana maraba da zuwan aminai daga kasashen duniya daban daban.(Lubabatu)