Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-07 22:22:51    
Membobin babban iyalin Olympics sun taru a nan birnin Beijing

cri

Saurari

A ran 7 ga wata da sassafe, tare da kide-kiden wakar wasannin Olympics, an shirya bikin hadin gwiwa na daga tutoci don kungiyoyin 'yan wasa na kasashen Afirka ta Kudu da Norway da dai sauransu a cikin kauyen 'yan wasannin Olympics na Beijing. Chen Jian, mai jarogancin bikin na kauyen ya bayyana cewa,

"Za mu yi iyakacin kokarinmu domin samar da hidima mafi kyau ga kungiyoyin 'yan wasa na kasashe daban daban. 'Duniya daya, buri guda' shi ne muhimmin take na gasar wasannin Olympics ta Beijing, muna fatan za a iya shimfida gadojin sada zumunci da kara fahimta tsakanin jama'a da kuma kasashe daban daban ta wannan gasar."

Bayan da birnin Beijing ya cimma nasarar neman samun iznin shirya wasannin Olympics na karo na 29 a shekara ta 2001, ya yi namijin kokari don shirya gasar. Yanzu Beijing ya riga ya yi shiri sosai a fannonin filaye da dakunan wasannin Olympics da ingancin iska da yawon shakatawa da kiwon lafiya da dai sauransu. Haka kuma yanzu kungiyoyin 'yan wasannin Olympics na kasashe da shiyyoyi kusan 200 sun riga sun shiga kauyen 'yan wasannin Olympics na Beijing. Bisa ka'idojin kwamitin wasannin Olympics na duniya, ya kamata a kammala bukukuwan daga tutocin dukkan kungiyoyin 'yan wasa a ranar kafin bikin bude gasar, kuma ba za a shirya bikin a ranar bude gasar ba. Bayan bikin daga tuta, Tubby Reddy, mataimakin shugaban kungiyar 'yan wasa ta kasar Afirka ta Kudu ya gaya wa wakilinmu cewa, yana sa ran alheri sosai kan gasar wasannin Olympics ta Beijing. Kuma ya kara da cewa,

"Wannan shi ne karo na hudu da na shiga wasannin Olympics, birnin Beijing wuri ne mafi kyau. Muna fatan 'yan wasanmu za su iya yin fintikau domin neman samun lambobin yabo a cikin gasannin ninkaya da guje-guje da kuma kwale-kwale."

A ranar kuma, baki manyan mutane sun sauko a filin jiragen sama na duniya na birnin Beijing bi da bi, ciki har da shugaban kasar Amurka Gorge W. Bush, da firayim ministan kasar Rasha Vladimir Putin da dai sauransu. Ba kawai sun zo Beijing ne tare da burinsu na wasannin Olympics ba, har ma suna mika hasken zuci da bege da duniya ke nuna wa ruhun Olympics. A ran 8 ga wata da dare, shugabannin kasashe fiye da 80 za su halarci bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing tare.

Ta yin amfani da damar shirya wannan gagarumin biki na wasannin Olympics na duniya, birnin Beijing ta nuna wa duniya sanannun wuraren shan iska da cike suke da sigogin gargajiya da kuma kayayyakin zamani. A gefen titin Chang'an na birnin, wakilinmu ya gamu da Tatiana Lebedeva da kuma mijinta da suka zo daga kasar Rasha. Wannan shi ne karo na uku da suka zo kasar Sin, kuma a wannan karo, sun zo Beijing ne don kallon wasannin Olympics. Madam Tatiana ta nuna yabo sosai ga sabuwar sifar birnin Beijing, kuma ta ce,

"Mun ga dimbin sabbin wuraren shan iska da filaye da ke da nasaba da wasannin Olympics, kuma halin annashuwa ya game ko ina. An shirya gasar wasannin Olympics sosai, kuma jama'ar Sin suna da hasken zuci kwarai. Muna son birnin Beijing sosai."(Kande Gao)