Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-07 17:17:05    
Mutanen Korea ta kudu suna cikin zaman jin dadi a kasar Sin

cri

Yan kasuwa na Korea ta kudu da suka zo birnin Qingdao na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin domin zuba jari da kafa masana'antu sai kara yawa suke a kwana a tashi,yanzu a birnin Qingdao aka fi samun yawan mutanen Korea ta kudu a kasar Sin. Aminanmu na Korea ta kudu suna cikin zaman jin dadi a kasar Sin har ma suna aiki tukuru sun zama wani kashi da ba iya raba shi da mutanen kasar Sin wajen bunkasa tattalin arziki na lardin Shandong.A cikin shirinmu na yau za mu zagaya da ku a birnin Qingdao, domin ku ga yadda mutanen Korea ta kudu suke zama da aiki a kasar Sin.

Muryar da kuka ji dazu waka ce da 'yan makarantar little Dragon Academy English Centre ta birnin Qingdao ta lardin Shandong suka rera tare da farin ciki. Makarantar nan tana dab da hanyar Yanerdao ta birnin Qingdao dake da 'yan makaranta sama da dari,yawancinsu sun zo ne daga iyalan mutanen Korea ta kudu. Bayan da suka kammala karatunsu na zaman yau da kullum,a kan yi musu horo da turanci.Lokacin da wakilin gidan rediyonmu ya kai ziyara a wannan makaranta,'yan makaranta suna magana da turanci da sinanci da kuma yaren asalinsu na Korea, suna baiwa juna labarai dangane zamansu da na iyalansu a nan birnin Qingdao na kasar Sin.Tare da fara'a wasu sun gabatar da aminansu na lasar Sin, wasu kuwa suna bayyana sabbin kayayyakin wasa da suka saye, wasu kuwa sun yi wasa gaban camera,abin daukar hoto na wakilin gidan rediyo na kasar Sin/Gaba daya suka ce " muna so gidajenmu a kasar Sin kwarai da gaske!"

A cikin yan shekarun baya, mutanen Korea ta kudu da suke aiki da zama a birnin Qingdao na kasar Sin sai kara yawa suke, a halin yanzu dai mutanen Korea ta kudu da suke zama a birnin cikin dogon lokaci sun wuce dubu dari, sun dauki birnin Qingdao a matsayin mahaifiarsu ne ta biyu.Lee Sung Hoon yaro ne mai yawan shekaru goma da haihuwa yana zama a birnin Qingdao tare da iyayensa,yanzu ya iya yarensu na asali na Korea ta kudu da turanci da kuma sinanci. Ya ce shi mutumin birnin Qingdao ne na gaskiya. "mamata ta ce ina birnin Qingdao ne tun ina cikin mamata.Bayan kwanaki dari da mamata ta haifi ni,na dawo nan birnin Qingdao. Ba mu da gida a Korea ta kudu. Duk lokacin da muka dawo Korea ta kudu, muna zama a gidan kakana. Ina so gidanmu a kasar Sin.dalili kuwa shi ne domin a kasar Sin kawai ina da gida.. Yaran Korea ta kudu a birnin Qingdao kamar Lee Sung Hoon sun yi yawa. Yawancinsu sun zo nan kasar Sin ne tuna suna kanana, wasu kuma aka haife su a kasar Sin. Sun sami aminai sinawa, sun yi wasa da kayayyakin wasa na kasar Sin, kuma suna kallon film carton na kasar Sin. Kasar Sin ba kasar waje ba ce gare su, kasar mahaifiyarsu.

Kara wa yaran Korea ta kudu dake zaman nan kasar Sin ilimin turanci, buri ne na Mr Yang Yong Kyu,shugaban makarantar little dragon academy English center. Yayin da ya bayyana dalilin da ya sa ya bude makaranta a birnin Qingdao na kasar Sin, Mr Yang Yong Kyu ya ce "ina da sha'anina a Korea ta kudu,aminana su kan yi zantawa da ni kan zuba jari a kasar Sin. Daga baya ni kaina na zo wurin nan domin yin bincike da samu bayanai, na gano yanayin wurin na da dadi, muhallin zuba jari ma na da kyau, ya fi dacewa da zaman mutanen Korea ta kudu,daga bisani na kuduri aniyar zuwa birnin nan na Qingdao."

Gidan Mr Yang Yong Kyu yana birnin Seoul,babban birni na kasar Korea ta kudu inda ya kafa wata makarantar 'yan mata. Kafin shekaru hudu da suka gabata, tare da matarsa ya zo birnin Qingdao na kasar Sin ya kafa makarantar little dragon academy English center. Wajen nada sunan makaranta ya yi tunani mai zurfi ya kuma karanta littattafai da bayanai da dama, daga baya ya zabi 'little dragon'. Mr Yang Yong Kyu ya bayyana cewa 

"tun shekaru aru are dragon tana alamanta kasar Sin. Ina so in kusanci wannan babban dragon. Yaran da suka karo ilimi su ma suna so su zama little dragon,nan gaba za su zama manya, haka kuma su manyan gobe na kasa. Ina fatansu zama dragon da ke tafiya cikin yanci a sararin samaniya bayan da suka girma, su ba da taimakonsu ga ci gaban kasa da zamantakewa.."

Mr Yang Yong kyu ya shafe shekaru hudu ya yi zama a birnin Qingdao na kasar Sin. Ya sami aminai sinawa da dama, ya kan yi zantawa da su in ya sami sarari ko sha ti tare ko yin wasan golf yana jin dadin zama a birnin. Ya sami dansa na farko a birnin Qingdao. A wannan shekara da muke ciki ya cika shekaru biyu da haihuwa..Mr Yang ya nada wa dansa sunan 'Yingmin',bisa ma'anar sinanci yana nufin mutumin mai bajinta da hikima. Ya yi fatan dansa kamar mutanen kasar Sin da na Korea ta kudu su nuna bajimta da hikima da yin aiki tukuru da neman samun cigaba.

Matar Yang sunanta Kwon Young Jin kamar sauran mata na Korea ta kudu suna da nagarta sosai. Tana aiki a makaranta tare da mijinta, kuma ta kula da yara da harkokin gida yayin da ta koma gida. Ta ce kafin ta zo nan kasar Sin ta damu sosai kan zama a kasar Sin. Muhalli na da kyau ? za mu iya dace da yanayi da abinci na kasar Sin,ko kuwa akwai matsalar tsaro ? tare da shakku da damuwa ta zo nan kasar Sin da mijinta. Bayan zamanta na shekaru hudu a kasar Sin.babu matsalolin da suka dame ta ko kadan. Ita ma ta sami aminai a birnin Qingdao, ta kuma yi magana da mai saida ganyayen ci sosai. Ta ce "kafin na zo kasar Sin abokanana sun gaya mini cewa zama a kasar Sin ba shi da sauki. Da na shafe 'yan watanni ina zama a birnin Qingdao na ji saukin zama a nan. Duk lokacin da na koma Korea ta kudu na yi zama na mako daya a can ina so in dawo kasar Sin."

Madam Kwon Young Jin ta ce da ta fara zama a birnin Qingdao, hankalinta bai kwanta kan abubuwan da ta saya a wurin ba, shi ya sa duk lokacin da ta koma Korea ta kudu, ta kan sayo abubuwa masu yawa na zaman yau da kullum ta kawo su a kasar Sin. Daga baya ta gano abubuwa a wannan birnin suna da inganci kuma ba su da tsada,ta iya sayo abubuwan da take so daga kasuwar Carifour da sauran manyan kasuwanni,ta ji saukin zama a kassar Sin.

Mr Yang Yong Kyu da matarsa dukkansu suna jin dadin zama a birnin Qingdao,ban da wannan kuma sukan kawo iyayen kowanensu daga Korea ta kudu zuwa kasar Sin bisa lokaci lokaci da su yi zaman gajeren lokaci a nan. A halin yanzu Mr Yang ya yi hayar dakunan zama, yana fatan saye wani gida a birnin Qingdao da iyalinsa mai mutane uku ke iya zama a cikin dogon lokaci.kuma yana so ya kafa karin makarantun horo sauran birane na kasar Sin. Ya ce asalinsa yana kasar Korea ta kudu,sha'aninsa yana kasar Sin.

Iyalai kamar na Mr Yang Yong Kyu sun yi yawa a birnin Qingdao na lardin Shandong na kasar Sin. Bisa kididdiga da aka yi,an ce kamfanonin da 'yan kasuwa nna Korea ta kudu suka kafa a daukacin lardin Shandong sun wuce dubu goma, daga cikinsu dubu shida suna birnin Qingdao. Jarin da 'yan kasuwa na Korea ta kudu suka zuba a lardin Shandong ya wuce dalar Amurka biliyan ashirin,wato ya dau kashi 57 bisa dari na daukacin jarin da 'yan kasuwa na Korea ta kudu suka zuba a kasar Sin gaba daya, lardin Shandong ya zama kawar cinikaya mafi girma ga kasar Korea ta kudu.

Mr Kim Sun heung,babban jami'in karamin ofishin jakadanci na Korea ta kudu a birnin Qingdao na kasar Sin, shi dan diplomasiya ne mai aminci. Kafin ya zo nan birnin Qing shi babban jami'I ne na karamin ofishin jakadanci na Korea ta kudu a birnin Shanghai na kasar Sin. Ya shafe shakaru sama da ashiri yana yin mu'amala da kasar Sin,za a iya cewa shi masani harkokin kasar Sin ne.yana da 'ya'ya uku. Biyu daga cikinsu an haife su ne a kasar Sin,daukacin iyalinsa yana kishin kasar Sin.

Babban jami'in karamin ofishin jakadancin Korea ta kudu Mr Kin Sun heung ya bayyana cewa mutanen Korea ta kudu suna so lardin Shandong ne sabo da yankin kasarmu na dab da Korea ta kudu da al'adunmu kusan daya ne da sauran abubuwa da dama. Ya ce "da akwai abubuwa makamanci da dama tsakanin al'adun Korea ta kudu da na lardin Shandong. Cikin dogon lokaci,al'adun Korea ta kudu ya samu tasiri daga lardin Shandong. Yanayi da dabi'u da al'adun abinci na lardin Shandong sun yi kamar na Korea ta kudu sosai,yankunan bangarorinmu biyu suna dab da juna. Mutanen Shandong su kan nuna gatanci ga baki tare da fara'a. mutanen Korea ta kudu suna iya zama a lardin Shandong hankali a kwance."

Mr Kim Sun heung,karamin jakada na Korea ta kudu a birnin Qingdao na kasar Sin ya ci gaba da cewa da akwai abubuwa makamanci da dama tsakanin al'adun Korea ta kudu da na kasar Sin, shi ya sa mutanen Korea ta kudu su saje cikin zamantakewar kasar Sin tare da sauki. Ci gaban kasar Sin da sauyinta su kan kawo tasiri ga Korea ta kudu a ko wane lokaci Ba da taimako ga mu'amalar da ake yi tsakanin kasashen nan biyu Korea ta kudu da kasar Sin a fannonin tattalin arziki da al'adu da sauran fannoni,burin aminan Korea ta kudu ne gaba daya.