Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-07 14:29:28    
An bude sansanin matasa na Olympics na shekarar 2008 a birnin Beijing

cri

A ran 6 ga wata, wato a lokacin kusantowar bude gasar wasannin Olympics ta Beijing, an bude sansanin matasa na Olympics na shekarar 2008 a birnin Beijing a hukunce. Babban take na wannan sansanin matasa na wannan karo shi ne 'matasa za su kago wata kyakkyawar makoma', matasa 480 da suka zo daga kasashe da yankuna 205 sun iso birnin Beijing, inda suka fahimci gasar wasannin Olympics da al'adun kasar Sin tare.

Shugaban hukumar wasannin Olympics ta birnin Beijing Mr. Liuqi, da sakatare na farko na kwamitin tsakiya na kungiyar matasa ta kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban zartarwa na hukumar da ke kula da harkokin sansanin matasa Mr. Lu Hao, da shugaban zartarwa na hukumar wasannin Olympics ta birnin Beijing Mr. Guo Jinlong, da kuma shugaba mai girmamawa na hukumar wasannin Olympics ta duniya Mr. Juan Antonio Samaranch su ma sun halarci bikin bude sansanin.

Mr. Liu Qi ya sanar da bude sansanin matasa.

Ya ce, 'Yanzu, ana bude sansanin matasa na wasannin Olympics na shekarar 2008 na birnin Beijing.'

Mr. Lu Hao ya ce, sansanin matasa na wannan karo ya dukufa wajen sa kaimi ga yin mu'amala da ke tsakanin matasa na kasa da kasa. Ya ce,'Sansanin matasa ya samar da wani muhimmin dandamali ga matasa na kasa da kasa da su koyi ilmi, da fahimci wasannin Olympics, da kara fahimtar juna da sada zumunta a tsakaninsu, haka kuma sansanin matasa yana da muhimmiyar ma'ana waje yada ra'ayoyin Olympics na hadin kai, da sada zumunta, da zaman lafiya, da sa kaimi ga yin mu'amala da ke tsakanin matasa na kasa da kasa, da kuma sada zumunta da ke tsakaninsu.'

A matsayin shugaba mai girmamawa a duk rayuwarsa na hukumar wasannin Olympics ta duniya Mr. Juan Antonio Samaranch ya taya murna ga matasa a bikin bude sansanin. Ya ce, 'Da farko, ni da kaina kuma a madadin shugaban hukumar wasannin Olympics ta duniya wato Mr. Jacques Rogge, na taya murna ga ko wanenku, ku taki sa'a. Na iya tabbatar da cewa, gasar wasannin Olympics ta Beijing za ta fi nuna kwarewa a duk tarihin Olympics. Tabbas ne mu nuna godiya ga abokanmu na kasar Sin, a sa'i daya kuma mu taya murna gare su. Ban da wannan kuma, ina nuna godiya ga hukumar wasannin Olympics ta Beijing, da kuma shugabanta Mr. Liu Qi. Za a bude gasar wasannin Olympics ba da dadewa ba, ina tsammanin kuna da buri daya kamar burina, wato muna fatan za a shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing cikin nasara.'(Danladi)