A gun bikin rufe gasar wasannin Olympics ta Sydney, wannan waka mai taken "Yin mafarki dn fuskantar kalulabanci" da shahararrun mawaka na kasar Australia suka rera ta shaku cikin zukatan mutane sosai. Daga baya kuma, wakar ta samu karbuwa sosai a duk duniya. Darren Yap, mataimakin darekta na bikin rufe gasar wasannin Olympics ta Sydney ya bayyana cewa, bikin rufe gasar ya sha bamban da na bude gasar. Ya kamata bikin bude gasar ya kasance gagarumi, amma kamata ya yi bikin rufe gasar ya nuna halin sakin jiki a gwargwado. Tun farko, suna son shirya bikin rufe gasar wasannin Olympics ta Sydney don ya zama wata babbar liyafa. Kuma Mr. Yap ya kara da cewa,
"Bikin rufe gasar da muka shirya ya yi kamar wata liyafar barbecue da a kan yi a farfajiyar bayan gidanka, wanda cike yake da halin musamman na kasar Australia. Haka kuma mun gayyaci dimbin sanannun mawaka iri na salon Rock, shi ya sa bikin rufe gasar ya yi kamar wani bikin taya murna da kuma bikin wakoki na salon Rock. Ko shakka babu, mu ma mun gayyaci 'yan wasa masu yawa duk saboda shi ne gasar wasannin Olympics. 'Yan wasa fiye da dubu goma da suka zo daga kasashe daban daban da kuma 'yan kallo na wurin sun yi wake-wake da raye-raye tare da mawaka iri na salon Rock na kasar Australia."
A idon Mr. Yap, al'adun kasar Sin suna da dogon tarihi da kuma abubuwan gargajiya, kuma sun dora muhimmanci kan iyali. Shi ya sa ya kamata bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing da na rufe gasar su hada da abubuwan gargajiya da na zamani tare, da kuma abubuwan gabashin duniya da na yammacin duniya tare. Ban da wannan kuma ya nuna cewa, wannan shi ne wani gagarumin bikin wasanni da aka shirya a karni na 21, shi ya sa tabbas ne bikin na da zamani. Kuma ya kara da cewa, "Idan na iya samun damar sa hannu a cikin ayyukan darekta na bikin bude da rufe gasar wasannin Olympics ta Beijing, zan mai da hankali kan abubuwan zamani, da kuma bayyana hasashen makoma na yara manyan gobe. Game da wakoki da zane-zanen da za a yi amfani da su, na fi sha'awar abubuwan da ke iya alamanta zamani."
Bugu da kari kuma, Mr. Yap ya bayyana cewa, ya yi imanin cewa, tabbas ne bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing da na rufe gasar za su jawo hankulan mutane sosai. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da bisa ka'idojin da aka saba bi, dole ne bukukuwan budewa da rufewa musamman ma bikin budewa ya nuna tarihin kasar da ta daukar nauyin shirya wasannin Olympics, kuma kasar Sin wata kasa ce mai wayewar kai da ke da tarihi fiye da shekaru dubu, shi ya sa tana iya nuna labarai iri daban daban. Kuma Mr. Yap ya kara da cewa, "Na yi imanin cewa, tabbas ne bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing zai nuna mana wani labari mai dadin ji kan tarihin kasar Sin na shekaru fiye da dubu, shi ya sa bikin zai kasance kamar wata gada ce da za a iya fahimtar abubuwan da suka faru a da, musamman ma fahimtar al'adun gargajiya na kasar Sin. Kuma Na yi zaton cewa, tabbas ne bikin bude gasar zai zama wani gagarumin biki ne. Game da bikin rufe gasar, ya yi kamar bikin rufe gasar wasannin Olympics ta Sydney, mai yiyuwa ne zai kasance kamar wani bikin wake-wake, inda za a iya samun dimbin mawaka na salon Popo da kuma abubuwan zamani. A gun bikin rufe gasar, ya kamata a fi mai da hankali a kan taya murnar shirya gasar cikin nasara da kuma nuna godiya ga 'yan wasa na kasashe daban daban."
|