Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-06 15:03:22    
Kafofin watsa labaru na kasar Kenya suna alla-allar bayar da labaru kan wasannin Olympics

cri

A ranar 8 ga wata za a bude wasannin Olympics na Beijing, manyan kafofin watsa labaru daban daban na kasar Kenya, wato wata kasar da ta fi girma wajen motsa jiki a Afrika, sun yi shirye-shirye iri daban daban, don bayar da labarai kan wannan gagarumin wasannin motsa jiki na dukkan duniya. Kwanan baya, wakilanmu sun kai ziyara ga wasu muhimman kafofin watsa labaru na kasar Kenya, inda wasu manema labaru da za su zo nan birnin Beijing suka bayyana ra'ayoyinsu kan wasannin Olympics. Yanzu kuma, bari mu ga cikakken bayanin da wakilanmu suka ruwaito mana daga kasar Kenya.

Kamfanin watsa labaru na kasar Kenya, wato KBC, shi ne kafar watsa labaru daya kawai daga kasar da ya samu amincewar ba da labari kai tsaye a duk lokacin wasannin Olympics. Ban da wannan kuma, kamfanin ya shirya wani shirin musammam na rediyo mai tsawon minti goma, da kuma wani shiri na talibijin mai tsawon minti talatin, har ma kullum yana jawo hankulan mutane da yawa.

Shugaban kamfanin KBC David Waweru ya bayyana cewa, yana fatan sanar da hasashen wasannin Olympics, da karfafa sada zumunci a tsakanin jama'ar kasashen Sin da Kenya ta hanyar ba da labari kan wasannin Olympics na Beijing. Ya ce,

"A ganina, kamar gasar cin kofin duniya ce, wasannin Olympics shi ma wani gagarumin wasan motsa jiki da ke jawo hankulan dukkan duniya. Yana da wani irin karfi wajen hada kan jama'ar kasashe daban daban na duniya. Yanzu, za a shirya wasannin Olympics a birnin Beijing, haka kuma ana zura ido kan kasar Sin, saboda wannan ne wata dama mai kyau wajen nuna wa duniya tarihin kasar Sin, da al'adunta, da bunkasuwar kasar ta zamani. Lallai ina jin farin ciki ne don bayar da labaru kan kasar Sin ga jama'ar kasar Kenya."

Bayan haka kuma, Mr. Waweru ya ce, bayan da aka bude wasannin Olympics, kamfaninsu zai yi shirye-shirye kai tsaye har na tsawon awa 6 a ko wace rana.

A waje daya kuma, wata kafar watsa labaru ta talibijin ta kasar Kenya, wato gidan talibijin na al'umma, ya aika da manema labaru biyu, wadanda suka kware wajen bayar da labaru kan wasannin motsa jiki da su zo nan kasar Sin, don bayar da labaru kan wasannin. Evelyn Watta, tana daya ce daga cikinsu. Ko da ya ke tana karkashin matsi daga ayyukanta sosai, amma jikinta ya tsumu sosai sabo da ziyarar da za ta yi a nan kasar Sin. Ta ce,

"Shiga ayyukan watsa labaru kan wasannin Olympics, wannan ne abin farin ciki gare ni, shi ne kuma buri na karshe na manema labaru a zaman rayuwar sana'arsu."

A kan mayar da hankali kan bayar da labari cikin lokaci wajen yin shirye-shirye na rediyon da na talibijin, amma a kan kula da yin bayani mai zurfi ta hanyar jaridu. A 'yan kwanakin da suka wuce, muhimman jaridu daban daban na kasar Kenya suna ta kara bayar da labaru kan wasannin Olympics. Yanzu, kwararren 'dan jaridar The Standard ta kasar Kenya Omulo Okoth yana nan kasar Sin, ya kuma fara ziyararsa. Ya bayyana kwarin gwiwarsa sosai kan wasannin Olympics na Beijing. Kafin tashinsa daga Kenya ya gaya wa wakilanmu cewa, 

"Wasannin Olympics na Beijing wata dama mai kyau ce wajen nuna kasar Sin ga dukkan duniya. Kyakkyawar al'adu na kasar Sin, da imanin da jama'ar kasar ke nunawa, da tsayawa tsayin dak da suke yi kan motsa jiki, da dai sauransu, dukkansu su ne jigogi masu kyau wajen bayar da labaru. Bayan haka kuma, a ranar bude wasannin Olympics zan rubuta muhimman lamarin da ke da nasaba da tarihin wasannin Olympics, don sanar da hasashen wasannin Olympics."