Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-06 09:10:20    
Ziyarar 'dan wasan kasar Tanzaniya Akhwari a kasar Sin

cri

A shekarar 1968, a gun gasar wasannin Olympic da aka shirya a kasar Mexico, 'dan wasan gudun Marathon daga kasar Tanzaniya John Stephen Akhwari ya taba jin rauni mai tsanani, amma bai bar gasa ba, sai ya ci gaba, a karshe dai ya isa wurin karshe. Halin nan na 'ba zai bari ba har abada' ya samu yabo sosai daga wajen jama'ar kasashen duniya. Yanzu, jarumin nan ya zo kasar Sin domin ziyarci dakuna da cibiyoyin wasannin Olympic na kasar Sin bisa gayyatar da gidan rediyon kasar Sin ya yi masa. A cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani kan wannan.

Bisa matsayinsa na bako daga Afirka, Akhwari ya samu karbuwa sosai a Beijing, kuma masu sa kai da yawan gaske za su gabatar da hidimomi daga dukkan fannoni ga 'yan wasa da masu yawon shakatawa da harsunan waje 55. Game da wannan, shugaban hukumar kula da aikin masu sa kai ta kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing Li Jian ya gaya mana cewa,  "Murmushin masu sa kai shi ne katin sana'a mafi kyau na Beijing, a gun gasar wasannin Olympic da gasar wasannin Olympic ta nakasassu na Beijing, gaba daya masu sa kai za su kai dubu dari daya, yanzu dai mun riga mun gama aikin share fage."

Akhwari shi ma ya ji farin ciki sosai saboda ya ji harshen Swahili a Beijing, ya ce:  "Masu aikin sa kai na gasar wasannin Olympic ta Beijing suna da kirki kuma sun nuna kwazo da himma kan aiki. Ko shakka babu 'yan wasa daga kasashe daban daban za su gamsar da aikinsu."

Akhwari ya nuna fatansa cewa, yana son ganin filin wasan motsa jiki mai siffar gidan tsuntsaye wato `Bird`s Nest` da idonsa, a karshe dai, ya cim ma burinsa. Da zarar ya shiga filin, sai ya ji mamaki sosai, ya ce: "Ya yi girma, kuma ya yi kyau, matsayin fasahar ginin ya kai matsayin koli a duniya, na hakake cewa, 'yan wasa da masu yawon shakatawa za su kaunarsa kamar yadda nake ji. A sa'i daya kuma, ina fatan 'yan wasan da za su yi gasa a nan za su samu sakamako mai gamsarwa kuma za su kago sabon matsayin bajimta a nan."

Daga baya kuma, Akhwari ya je birnin Qingdao wanda zai dauki bakuncin gasar tseren kwale-kwale domin gasar wasannin Olympic ta Beijing. Akhwari ya yabawa birnin sosai saboda matakan tsimin makamashin da ya dauka. Ya ce:  "Gine-ginen cibiyar tseren kwale-kwale ta Qingdao sun yi kyau, alal misali dakin kwana da dakin cin abinci da dakin hutu da kuma dakin motsa jiki, kowanen 'dan wasa yana iya motsa jiki a nan, 'yan wasa nakasassu su ma suna iya motsa jiki a ciki."

Ban da wannan kuma, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na Beijing yana mai da hankali sosai kan aikin kiyaye muhalli, saboda haka, Beijing ya dauki matakai a jere musamman domin wannan, alal misali, a kara dasa bishiya da ciyawa, kuma a kayyade tafiyar mota, ana iya cewa, yanzu ingancin muhalli da iska ya riga ya sami kyautatuwa a bayyane.

Zeng Yiyi, wata yarinya wadda ke da shekaru shida na haihuwa ta ce:  "A makarantar renon kananan yara, malamai sun gaya mana cewa, kamata ya yi mu kiyaye muhalli, kada mu zuba datti ko ina kamar yadda muke so. Yanzu Beijing yana da kyan gani sosai, bishiya da fure da ciyawa sun yi yawa, ina fatan baki da za su zo daga kasashen waje domin gasar wasannin Olympic za su ji dadi a Beijing."

Kowa ya sani, kirarin gasar wasannin Olympic ta Beijing shi ne "Duniya daya, buri daya", kamata ya yi jama'ar duniya mu yi kokari tare don tabbatar da gudanarwar gasar wasannin Olympic lami lafiya. (Jamila Zhou)