Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-06 09:08:05    
Antwerp ya yi kokarin shirya zama na 7 na gasar wasannin Olympic

cri

Yakin duniya na farko da aka yi shekaru hudu ana yinsa ya kawo babban tasiri ga Turai, mutane fiye da dubu goma sun mutu a cikin yakin, kuma yakin ya rushe birane da yawa, haka kuma yakin ya kawo mugun tasiri ga wasannin Olympic. A sanadiyar yakin, hedkwatar kwamitin wasannin Olympic ta kaura daga birnin Paris na kasar Faransa zuwa birnin Lausanne na kasar Switzerland, kuma an soke zama na 6 na gasar wasannin Olympic da aka shirin shirya a birnin Berlin na kasar Jamus a shekarar 1916. A karkashin irin wannan hali, ana shakkar cewa, ko za a iya ci gaba da shirya gasar wasannin Olympic? Amma birnin Antiwerp na kasar Belgium wanda ya haye wahalar yaki ba da dadewa ba ya ba mu amsa bisa hakikanin aiki.

A shekarar 1918, kwamitin wasannin Olympic na duniya ya bullo da cewa za a shirya zama na 7 na gasar wasannin Olympic, daga baya kuma birane uku sun gabatar da rokon shirya gasar, a karshe dai, kwamitin wasannin Olympic na duniya ya zabi Antwerp ya shirya zama na bakwai na gasar wasannin Olympic. A gun yakin duniya na farko, sojojin kasar Jamus sun kai hari kan birnin, kuma sun rushe gidajen kwana da masana'antu da yawan gaske, mazauna birnin da yawa sun rasa aikin yi, a karkashin haka, karamar gwamnatin birnin Antwerp da mazauna birnin sun yi iyakacin kokarin yin aikin share fage, kuma bayan watanni 18, sun gina wani filin wasannin Olympic mai daukan 'yan kallo dubu 30, a sa'i daya kuma, sun gina sauran filaye da gine-ginen wasannin motsa jiki bisa rokon kwamitin wasannin Olympic na duniya, alal misali, wurin wasan iyo da filin harbe-harbe da dai sauransu, ana iya cewa, Antwerp ya ba mu babban mamaki a tarihin shirya gasar wasannin Olympic.

Saboda dalilin yaki, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na birnin Antwerp bai gayyaci 'yan wasan kasar Jamus da sauran kasashe da su halarci wannan zama na gasar wasannin Olympic ba, shi ya sa ake ganin cewa, gasar wasannin Olympic ta Antwerp ba cikakkiyar gasa ba ce. Amma a hakika dai, yawan 'yan wasan da suka shiga gasar ya fi yawa a tarihin wasannin Olympic, wato 'yan wasa fiye da 2500 daga kasashe 29 sun halarci gasannin da aka shirya musu a Antwerp. Ban da wannan kuma, an kara wasanni a gun gasar nan, alal misali wasan kokawa da wasan dambe da wasan hoki a fili da wasan daukan nauyi da sauransu. Abu mai ban sha'awa shi ne an shirya wasan kankara salo-salo da wasan hoki kan kankara a gun wannan zama na yanayin zafi na gasar wasannin Olympic.

A karkashin kokarin gwamnatin kasar Belgium da goyon bayan sauran kasashe, gasar wasannin Olympic ta Antwerp ta ci nasara. (Jamila zhou)