Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-05 20:10:34    
Wurin yawon shakatawa na gandun daji na Olympic a Beijing

cri

Masu sauraro, muna muku godiya da ci gaba da sauraren shirinmu game da filaye da dakunan wasa na taron wasannin Olympic na Beijing. Yau ma za mu gabatar muku da wani filin wasa na musamman.

Ko shakka babu hada wasan Olympic da kyan karkara na gandun daji tare wani ra'ayi ne mai kyau. Haka kuma kallon gasanni na matsayin koli a cikin gandun daji ya iya faranta mutane rai. A shekara mai zuwa, za a yi gasannin harbar kibiya da wasan kwallon tennis da kwallon gora a fili na taron wasannin Olympic na Beijing a cikin irin wannan wurin yawon shakatawa a birane.

A arewancin birnin Beijing, akwai wani 'wuri' da aka dasa bishiyoyi da ciyayi da yawa a wajen, shi ne wurin nisadi na gandun daji na Olympic.

An fara gina shi a ran 30 ga watan Yuni na shekarar 2005. Fadinsa ya kai misalin kadada 680. Filin kwallon gora a fili da filin harbar kibiya da kuma cibiyar wasan kwallon tennis suna kudancin wannan wurin yawon shakatawa. Fadin filin kwallon gora a fili ya kai misalin kadada 11.87, a cikin sassansa guda 2 akwai kujeru dubu 17. A cikin filin harbar kibiya mai fadin misalin kadada 9.22, akwai kujeru dubu 5. Sa'an nan kuma, za a kafa filayen wasa 10 da kuma filayen wasa na hora 6 a cikin cibiyar wasan kwallon tennis, inda akwai kujeru dubu 17 da dari 4 a ciki gaba daya. Filin kwallon gora a fili da filin harbar kibiya filayen wasa ne na wucin gadi, bayan taron wasannin Olympic na Beijing, za a maido da dasa ciyayi a kansu. Sai cibiyar wasan kwallon tennis ne kacal za a ci gaba da amfani da ita a matsayin sansanin horar da 'yan wasan kwallon tennis na kasar Sin da kuma wurin yin wasa da kwallon tennis ga 'yan birnin.

Babban take da aka tsara wajen zayyana wurin yawon shakatawa na gandun daji na Olympic shi ne an hade kayatar da birni da kuma muhallin halittu gaba daya yadda ya kamata, ana nufin nuna wa 'yan birni gandun daji.

Don yin iyakacin kokari wajen rage illar da harkokin mutane ke kawo wa muhallin halittu a wannan wurin yawon shakatawa, da samar da kyakkyawar yanayi ga wannan wurin yawon shakatawa, masu zayyana sun fito da shirye-shiryen musamman. Ga misali da dare ana kiyaye sararin sama a yayin da aka kunna fitilu, ta haka za a kare dabbobin dare, sa'an nan kuma, mutane na iya kallon taurari a birnin.

Yanzu an kammala dasa ciyayi a galibin bangaren arewa na wurin yawon shakatawa na Olympic, a bangaren kudu kuwa, an kammala dasa ciyayi har da kashi 80 cikin kashi dari. Haka kuma, a galibi dai ana iya ganin kayatawar bishiyoyi a wajen. Babu tamtama tabbas ne za a kashe dogon lokacin wajen samar da kyakkyawan tsarin halittu masu rai a cikin wani wurin yawon shakatawa na gandun daji da mutane suka gina, haka kuma, irin wannan wurin yawon shakatawa na gandun daji zai taka rawa bayan taron wasannin Olympic sannu a hankali, zai kyautata ingancin iskar Beijing a kwana a tashi. Ban da wannan kuma, a matsayin wuri mai dimbin bishiyoyi da ciyayi da ya hada birane da wuraren bayan gari, zai sassauta yanayin zafi a birnin, zai zama huhun Beijing wajen fito da iska mai tsabta.