Nuna ire-iren al'adun duniya wani buri ne na gwamnatin kasar Sin wajen shirya dimbin harkoki a lokacin gasar wasannin Olympics. Ding Wei, wani jami'in ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ya gaya mana cewa, "Kwararru dubu 20 a fannin wasannin fasaha za su tattara a birnin Beijing domin bayyana babban ci gaba da duniya da kuma zamantakewar al'ummar kasar Sin ke samu a fannin ala'du. Ta harkokin al'adu na wasannin Olympics na shekarar bana, abokai da suka zo daga kasashe daban daban za su fahimci wata kasar Sin mai wayewar kai, wadda take mai da hankali a kan gadon gargajiya da kuma kirkire-kirkire, da kuma dora muhimmanci kan halayen musamman na kabilu da kuma al'adun duniya iri daban daban." 1 2
|