Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-05 15:43:45    
An bude cikakken taron kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa a birnin Beijing

cri
Jiya da dare, an bude cikakken taron kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa a karo na 120 a nan birnin Beijing, wanda ya kasance wani muhimmin taro kafin wasannin Olympics na Beijing.

An bude taron ne a gidan wasan kwaikwayo na kasar Sin da ke nan birnin Beijing. A madadin gwamnatin kasar Sin da jama'arta biliyan 1 da miliyan 300 ne, shugaba Hu Jintao na kasar, wanda ya halarci bikin bude taron, ya yi lale marhabin da wakilan kwamitin mahalartan taron, ya kuma nuna godiya ga kwamitin wasannin Olympics na duniya, ya ce, "Tun bayan da Sin ta koma wajen wasannin Olympics, kwamitin wasannin Olympics na duniya na nuna goyon baya sosai ga mu'amala da hadin gwiwar da ke tsakanin bangarorin biyu, wanda ya samar da taimako mai daraja ga bunkasuwar harkokin wasanni a kasar Sin. Musamman ma yayin da Sin ke neman karbar bakuncin wasannin Olympics da kuma share fagensa, kwamitin wasannin Olympics na duniya ya ba ta muhimmin jagoranci da kuma goyon baya daga fannoni daban daban, wanda ya tabbatar da ganin kome ya gudana kamar yadda ya kamata. Sabo da haka, da sahihiyar zuciya ne nake godiya ga shugaba Jacques Rogge da kuma wakilai daban daban na kwamitin wasannin Olympics na duniya."

Mr.Hu Jintao ya kuma sake bayyana alkawuran da Sin ta dauka wajen gudanar da wasannin Olympics, ya ce, "Gudanar da wasannin Olympics na Beijing da ke da halinsa na musamman kuma yadda ya kamata, muhimmin alkawari ne da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suka dauka a gaban gamayyar kasa da kasa. Muna fatan ta hanyar gudanar da wasannin Olympics, za a iya kara bunkasa wasannin Olympics a duniya, kuma a kara yada manufar wasannin Olympics, sa'an nan, a kara bunkasa hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashe daban daban a wajen wasanni da dai sauran fannoni daban daban, a kara bayyana burin jama'ar Sin na jin dadin cigabansu tare da jama'ar kasashe daban daban da kuma bude makoma mai kyau."

A gun taron, shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya, Jacques Rogge ya nuna godiya ga gwamnatin Sin da jama'arta sabo da babban kokarin da suka yi wajen share fagen wasannin Olympics, ya ce, "Wasannin Olympics sun zo kasar Sin, wadda ke da kashi 1/5 na mutanen duniya, abin shi kansa na da ma'ana sosai. A ran Jumma'a mai zuwa, mutane kimanin biliyan 1 za su kalli bikin bude wasannin Olympics a gaban telebijin. Wasannin Olympics na Beijing za su taimaka wajen cimma burin yada wasannin Olympics da takara da juna cikin adalci. Ina da imanin cewa, wasannin Olympics za su bai wa kasar Sin wani kayan tarihi mai daraja. kasar Sin na da makoma mai kyau, tana da karfi sosai, kuma tana fuskantar kalubale. Wasannin Olympics na 2008 za su zama wata ishara a wajen bunkasuwar kasar Sin."

Ba da jimawa ba, za a fara wasannin Olympics a birnin Beijing. A gun bikin bude taron, shugaban kwamitin wasannin Olympics na Beijing, Mr.Liu Qi ya ce, Beijing a shirye take."A halin yanzu, sakamakon wasannin Olympics da kuma irin halin musamman na gargajiya kuma na zamani na birnin Beijing, Beijing ta riga ta zama birni na wasanni da birni na al'adu kuma birni na Olympics. Dukannin filayen wasa da na'urori da kuma ma'aikata a shirye suke, kuma masu aikin sa kai da mazauna birnin Beijing suna maraba da zuwan 'yan wasa da aminai daga nahiyoyi biyar. Muna iya alfaharin cewa, Beijing a shirye take."(Lubabatu)