A lokacin kuwa suna sanya tufafi masu launuka daban-daban, kuma suna sanya kayan ado da aka yi da azurfa daga kawuna har zuwa kafafuwansu, kuma sukan daga kwafofin giya don yin fatan bakin za su sha giya ta kwaf daya, kuma za su manta da gajiyar da suke ji sabo da doguwar tafiya. To, jama'a masu sauraro, cikin shirinmu na yau na "Kananan kabilun kasar Sin", za mu kai ku ziyara don fadakar da ku imanin da 'yan kabilar Miao suka bayyana cikin hotunan da aka zana a kan tufafinsu da kayan ado da suke sanya.
Kabilar Miao tana daya daga cikin kananan kabilu 55 na kasar Sin, yawancinsu suna zama a ladunan Guizhou da Yunan da Hunan.
A garin Xijiang na gudumar Leishan ta yankin kabilar Miao da ta Tong da ke kudu maso gabashin lardin Guizhou, da akwai wani kauyen inda iyalan 'yan kabilar Miao fiye da 1,000 ke zama. A nan wakilinmu ya gane cewa, malam bude littafi shi ne abun da aka zana siffarsa mafi yawa a kan tufafin mutane. Wani shugaban iyalan kabilar da ke zama a nan wanda sunan babansa Tang ya bayyana cewa,
"Hotuna mafi yawa da aka zana a kan tufafi ko kayan ado na azurfa da muke sanya su ne malam bude littafi. An ce kakanninmu malam bude littafi ne, sabo da haka muna nuna girmamawa gare su, kuma mukan kira su da sunan "uwaye malam bude littafi."
'Yan kabilar Miao suna kishin halittu masu rai kuma suna nuna musu girmamawa, sabo da haka sukan bayyana abubuwan da suke kauna a kan tufafinsu ko kayan ado na azurfa da suke sanyawa a jikunansu, ban da hotunan malam bude littafi, kuma da akwai na tsuntsaye da mamun daji da furanni da kifaye da na kwari ciki har da dodanni da jemagu, hotunan da aka zana suna da kyaun gani kuma masu ban sha'awa, yawancin abubuwan halittu da aka zana suna da ma'anar yin hayayyafa, da yin zama tare, da samun 'ya'ya da yawa, kuma da zaman alheri da wadata, da samun bunkasuwa.
Kafin 'yan mata na kabilar Miao suka yi aure, tabbas ne su da kansu suka yi kwado da linzami a kan tufafin da za su sa a ranar aure.
Ban da tufafi masu kyaun gani da aka yi musu kwado da linzami, kayan ado da aka yi da azurfa kuma sun zama wani abu daban da jama'a 'yan kabilar Miao suka dauka don bayyana tarihinsu da imaninsu. Abubuwan da 'yan kabilar Miao suka sassaka kan kayan ado na azurfa sun yi kama da na kwado da linzami da aka yi a kan tufafi, yawancinsu malam bude littafi ne, kuma da sauran hotunan dabbobi ko tsire-tsire wadanda 'yan kabilar Miao ke nuna girmamawa gare su. Alal misali kahon azurfa da 'yan mata suke sanyawa a kawunansu, wata irin al'ada ce da ake gadar tun shekaru aru-aru wato tun lokacin da kabilar Miao take cikin zaman al'umma na mata. A wancan lokaci, maza 'yan kabilar Miao suna son zama masu kuzari, sabo da haka dukansu sun sa kahonin shanu a kawunansu, kuma sun mai da kahonin shanu a matsayin makaman fada, daga baya mata 'yan kabilar Miao su ma sun bi sawon maza, kuma sun mai da kahonin shanu da su zama alamun kayan ado wato kahonin da aka yi da azurfa.
Daidai kamar yadda tufafi masu kwado da linzami kuma masu kayatarwa, kayan ado da aka yi da azurfa su ma sun zama daya daga cikin kayayyakin aure ga 'yan mata na kabilar Miao, daga cikin wadannan kayayyakin aure na azurfi har da kaho da hula da furanni da 'yan kunne da matsefi da zobba da kawanyar wuya, duk nauyinsu ya wuce kilo 15. Madam Shen Aiqun, ma'aikaciyar hukumar furofaganda ta gundumar Taijiang ta yankin kabilar Miao da ta Tong da ke kudu maso gabashin lardin Guizhou ta bayyana cewa,
"Idan wani iyali yana da diya, wadda tun da take yarinya iyayenta suka fara shirya mata kayayyakin aure da aka yi da azurfa, ciki har da warwaro da kawanyar wuya da kuma kayan ado da aka sanya a kawunansu."
|