Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-04 21:57:44    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- tsakiyar watan Yuni na wannan shekara, an riga an fara kyautata hanyar mota da ta hada garin Dushanzi da gundumar Kuche na jihar Xinjiang ta kasar Sin, bayan shekaru 2 masu zuwa, wannan hanyar motoci da ta hada kudanci da arewacin tsaunin Tianshan za ta zama wata muhimmiyar hanyar da za a bi wajen yin sufuri a duk shekara.

An shimfida hanyar motoci da ta hada garin Duzhanzi da gundumar Kuche a shekaru na 70 na karnin da ya wuce, yawancin tsawon hanyar tana tafiya cikin tsaunuka da kwaruruwa. Bayan da aka shafe shekaru fiya da 10 ana amfani da wannan hanya mota wajen yin sufuri, kuma ga lalacewar da ta yi sabo da zaizayewar kasa da duwatsu da kankara, shi ya sa zirga-zirgar motoci ta tsaya cika. Yanzu akan yi amfani da wannan hanyar motoci cikin watanni 5 ko fiye a kowace shekara.

Hanyar mota da ta hada garin Dushanzi da gundumar Kuche wadda aka ware kudin Sin kusan Yuan biliyan 3 don yi mata gyare-gyare, wadda kuma ta tashi daga garin man fetur mai suna Dushanzi da ke arewacin jihar Xinjiang, kuma ta sauka gudumar Kuche, duk tsawonta ya kai kilomita 378, bisa shirin da aka tsayar an ce, za a kammala aikin kyautata hanyar a watan Oktoba na shekarar 2010.

---- Bayan mu'amalar da aka yi kwanan baya a tsakanin hukumomin yaki da miyagun kwayoyi na jihar Xinjiang ta kasar Sin da na kasar Pakistan, an kafa hadadden tsarin aiki a tsakaninsu domin magance sumogar miyagun kwayoyin da ake yi a wani wurin da ake kira Golden Crescent, ta yadda za a daidaita matsalar sumogar miyagun kwayoyi wadda sai kara tsanani take a kowace rana a wannan wuri.

Bayan da aka yi shawarwari a tsakanin bangarorin 2, an tsai da cewa, idan wani gefe ya yi aikin cigiyar miyagun kwayoyi, ya kamata ya sanar da gafe daban aikinsa a rubuce, idan wani gefe yana son samun taimako daga gefe daban, dole ne ya ba shi. Sa'an nan kuma an kafa tsarin yin mu'amalar juna tsakanin bangarorin 2 ta wayar tarho.

Jihar Golden Crescent tana bakin iyakar kasa da ke tsakanin kasashe 3 wato Afganistan da Pakistan da kuma Iran, siffar wannan wuri tamkar wani sabon wata, yanzu kuwa wannan wuri ya riga ya zama wurin da ke fitar da miyagun kwayoyi mafi yawa ga kasar Sin.