Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-04 21:54:27    
Ruhun gasar wasannin Olympics yana da daraja kwarai

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na "Gasar Olympics ta Beijing a idon jakadun kasashen duniya da ke nan kasar Sin". Ni Sanusi Chen ne ke jan akalar wannan shiri. A farkon mako na watan Mayu, an soma sayar da tikitin gasar wasannin Olympics ta Beijing a mataki na 3. Kamar sauran mutane suke yi, Mr. Amos Nadai, jakadan kasar Isra'ila da ke nan kasar Sin ya kuma kama tashar shafin internet ta gasar wasannin Olympics ta Beijing domin neman damar sayen tikitocin da yake so. Yana fatan zai iya sayen wasu tikitoci domin iyalinsa da abokansa da suke son kallon gasar wasannin Olympics ta Beijing.

"Na sayi tikitin gasar wasannin Olympic ta Beijing a kan shafin internet ba domin ni kadai ba, iyalana da yawa za su zo, sabo da haka, ina kokarin sayen dimbin tikitin gasar."

A watan Agusta na shekarar da ta gabata, Mr. Amos Nadai dan shekaru 60 da haihuwa ya hau kan mukamin jakadan kasar Isra'ila a nan kasar Sin, shi ne jakada na shida bayan da aka kafa huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Isra'ila tun daga shekarar 1992. Ya taba yin aiki a ofisoshin jakadancin kasar Isra'ila da ke kasashen Japan da Thailand da Norway. Ko da yake bai kai shekara 1 ba bayan da ya iso nan kasar Sin, amma ya riga ya kai ziyara ga biranen Changsha da Harbin na kasar Sin, kuma ya taba ganawa da wakilan kafofin watsa labaru na kasar Sin har sau da yawa, har ma ya bakunci wasu sanannun tasoshin internet na kasar Sin bisa gayyatar da aka yi masa. Sabo da haka, ana kiran shi cewa shi wani dan diplomasiyya ne da ke da sha'awar yin mu'ammala da 'yan jaridu. A waje daya kuma, abin da ya fi muhimmanci shi ne yana da sha'awa sosai kan wasannin motsa jiki. Sabo da haka, birnin Beijing da ke cikin shekara ta 2008 yana da wata ma'anar musamman daban a gare shi. Mr. Amos Nadai ya ce, "Lokacin da nake saurayi, ni wani dan wasa ne, kuma na taba halartar gasanni sau da yawa. Kuma ina da sha'awar kallon gasannin wasannin motsa jiki, kamar su gasannin wasan kwallon kafa da na raga. Ina tsammani ni wani mutum ne da ke da sha'awa sosai kan wasannin motsa jiki."

Abin da ya sanya Mr. Amos Nadai da ya yi farin ciki shi ne, zai iya kallon yadda 'yan wasannin motsa jiki na kasar Isra'ila za su halarci gasar wasannin Olympic a nan birnin Beijing. Yana alfahari sosai, kuma wannan hanya ce mafi kyau wajen taya shi murnar cika shekara daya da ya hau kan mukamin jakadan kasar Isra'ila a nan kasar Sin.

Mutane da yawa sun san kasar Isra'ila sosa, amma mai yiyuwa ne ba ku san wasannin motsa jiki na kasar Isra'ila sosai ba. A hakika dai, a kasar Isra'ila wadda yawan mutanenta bai kai miliyan 7 ba tana kwarewa sosai wajen wasannin motsa jiki, musamman a gun gasannin wasannin Olympic da aka yi a cikin 'yan shekaru nan da suka gabata, 'yan wasa na Isar'ila sun samu lambobin yabo kwarai. Alal misali, a gun gasar wasannin Olympic ta Barcelona da aka yi a shekarar 1992, a karo na farko ne 'yan wasa na Isra'ila sun samu lambobin yabo. Kuma a gun gasar wasannin Olympic ta Athen da aka yi a shekara ta 2004, a karo na farko ne Gal Friedman, dan wasan tseren kwale-kwale na yin amfani da karfin iska ya samu lambar zinariya domin kasar Isra'ila.

Mr. Amos Nadai ya ce, kasar Isra'ila za ta aika da 'yan wasannin motsa jiki kimanin 40 zuwa gasar wasannin Olympic ta Beijing, kuma za su yi kokarin neman lambobin yabo a gun gasar.

"A hakika dai muna fatan dukkan 'yan wasa da za su halarci gasar wasannin Olympic ta Beijing 'yan wasa mafi nagarta ne na kasarmu. Mun tsai da burin cin wasu lambobin yabo a gasannin wasannin Judo da tennis da wasan tseren kwale-kwale na yin amfani da karfin iska. An sani cewa, kasar Isra'ila tana bakin tekun Mideterranean, kuma muna da nagartattun 'yan wasan tseren kwale-kwale na yin amfani da karfin iska. Sabo da haka, muna fatan za mu iya samun wasu lambobin yabo a cikin gasannin wadannan wasanni."

Kwamitin Olympic na kasar Isra'ila ya tsai da ma'auni mai tsanani sosai domin zaban nagartattun 'yan wasa da su halarci gasar wasannin Olympic ta Beijing. A waje daya kuma, a kwanan baya, kwamitin Olympic ta Isra'ila ya sanar da cewa, za a samar da kudin yabo ga 'yan wasa na kasar da za su samu lambobin yabo a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing, wato, idan wani dan wasa ya samu lambar zinariya, zai iya samun kudin yabo kimanin dalar Amurka dubu 140, wanda ya samu lambar azurfa zai samu kudin yabo kimanin dalar Amurka dubu 70, kuma wanda ya samu lambar tagulla zai samu lambar yabo kimanin dalar Amurka dubu 47.

Haka kuma, a bayyane ne Mr. Amos Nadai ya ce, idan za a iya samun lambobin yabo, wannan abu ne mai kyau, amma ruhun Olympic yana da ma'ana daban. "Game da ruhun Olympic, a ganina, ya kasance da ma'ana biyu. Da farko dai, ko shakka babu wasanni mafi jawo hankulan mutane sosai. A waje daya kuma, abin da yake kuma da muhimmanci shi ne, kowa zai iya halarta, kuma sada zumunta a tsakanin 'yan wasannin motsa jiki da kafofin watsa labaru da wadanda suke kallon gasar. Ina fatan za a cimma wadannan buri biyu cikin nasara a cikin wannan gasar wasannin Olympic da ake yi a lokacin zafi."

Ruhun tabbatar da zaman lafiya da sada zumunta na Olympic yana da daraja sosai a gare kasar Isra'ila wadda ta sha yake-yake da yawa. Shekarar da muke ciki shekara ce ta cikon shekaru 60 da kafuwarta. A cikin wadannan shekaru 60 da suka gabata, an taba ta da manyan yake-yake 5 tare da sauran kananan rikice-rikicen da ba a iya kidaya adadinsu ba. A gun gasar wasannin Olympic da aka yi a karo na 20 a birnin Munich na Jamus a watan Nuwamba na shekarar 1972, 'yan wasanni 11 na kasar Isra'ila sun mutu sakamakon farmakin da wasu masu tsirarrun ra'ayoyi suka kai musu. Wannan hadari ya girgiza dukkan duniya, kuma ya zama abin bakin ciki da yake kasancewa a zukatan 'yan kasar Isra'ila har abada.

Har yanzu, kafin a kaddamar da gasar wasannin Olympic a kowane karo, 'yan wasanni na kasar Isra'ila suna shirya bikin nuna jana'izza ga takwarorinsu da suka mutu a cikin wannan hadari.

Wata matsala daban da yake-yake da rikice-rikice masu tsanani suka kawo kasar Isra'ila ita ce, mutane masu dimbin yawa sun zama nakasassu. Sabo da haka, cikin dogon lokacin da ya gabata, gwamnatin Isra'ila ta mai da hankalinta sosai kan wasannin motsa jiki na nakassasu. Mr. Amos Nadai ya kuma tabo batun da ke da nasaba da wasannin motsa jiki na nakassasu.

"Likita Ludwig Guttman, wani dan kasar Jamus ne ya kirayi a shirya gasar wasannin Olympic ta nakassasu lokacin da ake shekaru 40 na karnin da ya gabata. Bayan da kasar Isra'ila ta sami 'yancin kai a shekarar 1948, ba tare da bata lokaci ba, an gayyaci wannan likita da ya zo kasar Isra'ila. Sabo da mutane masu dimbin yawa sun ji raunuka a cikin yake-yaken neman yancin kai, kuma wasu daga cikinsu sun zama nakassasu. Nan da nan ne an gano cewa, wasannin motsa jiki suna da muhimmanci sosai ga aikin sake gina jikin nakassasu, musamman sake farfado da lafiya a cikin zukatansu. Wannan ya kuma sanya nakassasu da yawa da su shiga wasannin motsa jiki na nakassasu."

Yanzu, an riga an kafa wasu kulob na wasannin motsa jiki domin nakassasu a birane da yawa ciki har da birnin Tel Aviv da Haifa. A gun gasar wasannin Olympic ta nakassasu da sauran gasannin wasannin motsa jiki na nakassasu da aka shirya, 'yan wasannin motsa jiki nakasassu na Isra'ila sun samu makamako mai kyau har sau da yawa.

Ko da yake ya rage sauran 'yan kwanaki kafin gasar wasannin Olympic ta Beijing, amma Mr. Amos Nadai ya soma yin zato a cikin zuciyarsa cewa, tabbas ne za a shirya wani bikin kaddamar da gasar wasannin Olympic ta Beijing musamman a ran 8 ga watan Agusta ga duk duniya. Game da Zhang Yimou, babban direktan shirya bikin bude da rufe gasar, Mr. Amos Nadai yana cike da imani. Ya ce, "A ganina, shi gwani ne. Na taba kallon fim da yawa da ya yi, ciki har da 'Rataya tifilu masu launin ja' da 'jarumai' da 'neman kasancewa a duniya' da dai makamantansu. Abubuwan fim da ya yi su kan burge zukatan mutane da yawa. Na iya tunawa da wasu fim da ya yi duka, ko kide-kiden fim da ya yi. Sabo da haka, ina cike da imani cewa, bikin kaddamar da gasar wasannin Olympic ta Beijing zai burge zukatan duk duniya."

A cikin wannan shekara daya da ta gabata, da idonsa ne Mr. Amos Nadai ya gani saurin shirya gasar wasannin Olympic da birnin Beijing yake samu a fannonin gina dakuna da filayen wasannin motsa jiki da shimfida hanyoyin jirgin kasa da ke karkashin kasa. Ya amince da cewa, gasar wasannin Olympic na karo na 29 da birnin Beijing zai shirya za ta zama wata gasar wasannin Olympic mai jawo hankulan mutane sosai. "Shekara ta 2008 wata muhimmiyar shekara ce a gare kasar Sin. Ina fata kuma ina da imani cewa, wannan gasar wasannin Olympic da kasar Sin take shiryawa za ta zama wata gasar wasannin Olympic mafi jawo hankulan mutane."

Mr. Amos Nadai ya kara da cewa, gasar wasannin Olympic za ta zama wata kyakkyawar damar sanin kasar Sin a gare jama'ar Isra'ila. Jama'ar kasar Isra'ila za su ji mamaki ga abubuwan da kasar Sin, mai masaukin wannan gasa ta yi.

Yanzu, jakada Amos Nadai yana kokarin koyon harshen Sinanci. Yana fatan mutane da yawa za su iya sauraran fatan alheri daga bakinsa lokacin da ake gasar wasannin Olympic.

"Jama'ar kasar Isra'ila suna taya birnin Beijing da ya shirya gasar wasannin Olympic ta shekara ta 2008 cikin nasara. Sa kaimi kasar Sin."