Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-04 20:06:08    
An mika wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing a lardin Sichuan tare da farin ciki da hasken zuci

cri

Bayan kwanaki 83 da aukuwar mummunar girgizar kasa mai karfin digiri 8 bisa ma'aunin Richter a lardin Sichuan a ran 12 ga watan Mayu, an kaddamar da mika wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing ta karo na 29 a lardin Sichuan, kuma birnin Guang'an shi ne zango na farko. Jama'ar Sichuan da suka sake farfadowa a kan kangaye sun yi marhabin da zuwan wutar bisa ruhunsu na sa rai da kuma karfafa zuciya. To yanzu ga cikakken bayani.

Ban da birnin Beijing, lardin Sichuan zango ne na karshe wajen mika wutar gasar wasannin Olympics. Domin daina kawo cikas ga ayyukan sake farfadowa na yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa, kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ya magance yankunan da ke fama da bala'i mai tsanani lokacin da yake sake tabbatar da hanyar mika wutar a lardin Sichuan. Ko da haka, mazaunan wurin sun kunna hasken zuci sosai domin zuwan wutar gasar wasannin Olympics. Zheng Wenlong, wani dan birnin Chengdu na lardin ya bayyana cewa, ba kawai wutar ta kawo wa jama'a masu fama da bala'in farin ciki da kuma hasken zuci ba, har ma abu mafi muhimmanci shi ne ta karfafa zukatan jama'ar wajen sake raya gidajensu. Kuma ya kara da cewa, "A hakika dai, ta hanyar mika wutar gasar wasannin Olympics, ana mika kauna da ke tsakanin mutane, kuma ana mika wani irin ruhu, ta hakan an mika mana karfi. Yanzu jama'a na dukkan fadin kasar Sin suna lura da halin da yankunan da ke fama da bala'in ke ciki. Mun nuna musu godiya da kulawa da kuma taimakon da suka ba mu, dole ne za mu sake raya kyawawan gidajenmu bisa hannayenmu."

Lokacin da ake fama da girgirzar kasa da kuma ceton mutane, an samu dimbin labarai masu burgewa wajen ceton mutane. Sabo da haka, an kara mutane 29 da suka bayar da babbar gudummowa a wannan fanni domin su zama masu rike da wutar gasar wasannin Olympcis lokacin da ake mika wutar a lardin Sichuan. Zheng Qiang, wani dan birnin Mianyang na lardin yana daya daga cikinsu. Kuma ya gaya mana cewa,

"Bisa halin da dukkan yankuna masu fama da bala'in ke ciki yanzu, ana iya gano cewa, sannu a hankali jama'a masu fama da bala'in sun riga sun iya yin zaman rayuwa da kuma aiki kamar yadda ya kamata. Kuma ta hanyar shimfida hanyoyi cikin gaggawa wandada aka katse su sakamakon girgizar kasa, yanzu an riga an sake farfado da zirga-zirga na dimbin wurare."

Bisa taimakon da sassa daban daban da kuma kasashen duniya suka bayar, ayyukan fama da girgizar kasa da ceton mutane da kuma sake farfadowa na lardin Sichuan sun samu nasara sosai. Fararen hula na lardin Sichuan suna raya gidajensu bisa ruhun karfafa zuciya da kuma sa rai. Madam Tang Li, wata 'yar birnin Chengdu ta gaya mana cewa,

"Lokacin da ake mika wutar gasar wasannin Olympics a sauran birane, mun gano cewa, jama'ar dukkan fadin kasar Sin sun samar da kudaden taimako gare mu, sun yi mana fatan alheri, wanda ya burge mu kwarai. Jama'ar Sichuan suna da kwazo da jar zuciya da kuma kwarin gwiwa, tabbas ne za mu yi namijin kokari wajen sake raya garinmu. Muna fatan za a mika wutar gasar wasannin Olympics lami lafiya, da kuma yin gasar yadda ya kamata."(Kande Gao)