A ran 1 ga wata, Mr. Tan Xuxiang, mataimakin direktan kwamitin tsara fasalin birnin Beijing ya bayyana cewa, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, birnin Beijing ya hada ayyukan share fagen wasannin Olimpic da tsara fasalin duk birnin sosai, sabo da haka an samu babban ci gaba wajen tsara fasali da gudanar da harkokin birnin.
A gun taron manema labarun da aka yi a wannan rana, Mr. Tan Xuxiang ya ce, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, birnin Beijing ya gudanar da tunanin manyan tsare-tsare na "sabon birnin Beijing, da sabuwar gasar wasannin Olimpic", ya sa kaimi ga aikin tsara fasalin birnin da garuruwa yadda ya kamata ta hanyar share fage domin wasannin Olimpic, kuma an tsai da shiri gaba daya wajen yin muhimman ayyuka da kyautata muhalli, sabo da haka an sa kaimi ga bunkasa birnin da garuruwa cikin daidaici. (Umaru)
|