Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-01 17:59:21    
Shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya karbi intabiyo da kafofin watsa labaru 25 na kasashen waje suka yi masa cikin hadin gwiwa

cri

Yau ran 1 ga watan Agusta, wato ya kasance saura mako guda da za a bude gasar wasannin Olympics ta Beijing. A ran nan a birnin Beijing kuma, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya karbi intabiyo da kafofin watsa labaru 25 na kasashen waje suka yi masa cikin hadin gwiwa, inda ya ba da amsoshi ga tambayoyin da manema labaru suka yi masa kan gasar wasannin Olympics ta Beijing da bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin.

'Gasar wasannin Olympics ta Beijing ta zama ta jama'ar kasar Sin ne, har ma ta zama ta dukkan jama'ar kasashen duniya. A madadin gwamnatin kasar Sin da kuma jama'ar kasar Sin, na yi maraba ga abokai da su zo birnin Beijing domin halartar gasar wasannin Olympics ko kallonta, na yi maraba ga manema labaru daga kasa da kasa da su watsa labaru kan gasar wasannin Olympics ta Beijing.'

Game da wasu suka sanya siyasa cikin gasar wasannin Olympics ta Beijing, Mr. Hu ya ce,

'Muna ganin cewa, sanya siyasa cikin gasar wasannin Olympics ba zai iya taimaka wajen daidaita matsaloli ba, har ma ya saba wa ra'ayin gasar wasannin Olympics, ya saba wa buri daya na jama'ar kasa da kasa, a karshe dai, zai lalata bunkasuwar gasar wasannin Olympics.'

'Duniya daya, mafarki daya' ya zama kirari na gasar wasannin Olympics ta Beijing, game da haka, Mr. Hu ya ce,

'Wannan kirari ya bayyana burinmu cikin sahihiyar zuciya. Wato jama'ar kasar Sin suna son kara yin mu'amala da hadin kai da jama'ar kasa da kasa bisa ra'ayin gasar wasannin Olympics, domin bude wani sabon shafi na gasar wasannin Olympics ta duniya, da kuma samar da wata kyakkyawar makoma ga dukkan 'yan Adam.'

Game da wasannin da ya fi so, Mr. Hu ya ce,

'Na fi so wasan kwallon tebur, da wasan iyo. Idan na iya zabi wani, zan zabi wasan kwallon tebur, amma ban iya cim ma wannan buri ba, sabo da an riga an tabbatar da 'yan wasa da za su shiga cikin wasannin kwallon tebur.'(Danladi)