Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-01 16:11:11    
Ziyarar Akhwari a kasar Sin

cri

A gun wasannin Olympics na Mexico da aka yi a shekarar 1968, John Stephen Akhwari, dan wasan gudun dogon zango na kasar Tanzania, ya yi iyakacin kokarin kammala gasar gudun marathon, duk da raunin da ya ji. Shi ne ya bayyana mana ma'anar wasannin Olympics. Yau shekaru 40 sun wuce, a gabannin wasannin Olympics na Beijing, wannan babban jarumi ya zo kasar Sin a matsayin bakon gidan rediyon kasar Sin.

Burin kowane dan wasa ne ya iya wakiltar kasarsa zuwa wajen wasannin Olympics, kuma kowane dan wasan da ya shiga wasannin Olympics na alla-alla ya zama zakara. Bayan da John Stephen Akhwari ya kammala gasar gudun marathon a gun wasannin Olympics na shekarar 1968, Akhwari ya gaya wa manema labarai cewa, "kasarmu da ke da nisan mil 7000 ne ta kawo ni nan, ba domin in fara gasa ba, amma don in kammala ta." A hakika, idan bai ji rauni ba, burin Akhwari ba kawai kammala gasar ba. "Burin da na yi kokarin cimmawa a gun wasannin Olympics na Mexico shi ne "samun nasara", amma sabo da dalili na yanayi, ban kware sosai ba. A lokacin, na yi tsammani, ko da yake ba zan iya zama zakara ba, amma dole ne in kammala gasar, sabo da ina wakiltar kasata. Burina a lokacin shi ne zama zakara."

Yanzu a Afirka, kungiyar 'yan wasan guje-guje da tsalle tsalle na kasar Tanzania na kokarin share fagen wasannin Olympics, suna son cimma burinsu a gun wasannin Olympics da za a soma yi. Shugaban kungiyar, Fransis John ya ce, "yanzu muna share fagen wasannin Olympics kamar yadda ya kamata, likitoci ma a shirye suke, suna sa ido a kan lafiyar jikin 'yan wasa. Ina ganin kowa na da lafiya sosai. Burinmu da mafarkinmu shi ne samun lambobin yabo."

A lokacin da ya tabo magana a kan Akhwari, tsohon amininsa, Fransis John ya yi godiya ya ce, "gaskiya Akhawari ya ba mu taimako sosai, ya kware sosai a wajen wasannin guje-guje da tsalle tsalle, mun tattauna da shi, ya ba mu shawarwari da dama game da horar da 'yan wasa. Kafin ya tashi zuwa kasar Sin, ya taba zuwa birnin Arusha, mun yi hira, ya karfafa mana gwiwa. Karfin zuciyarsa ya jagoranci 'yan wasanmu su yi ta ci gaba, su haye wahalhalu, su cika burinsu."

Shugaban kwamitin wasannin Olympics na Tanzania, Gulam Abdalla, shi ma yana cike da buri mai yawa ga kungiyar 'yan wasan kasar Tanzania da za su tashi zuwa wasannin Olympics. "Za mu shiga gasanni uku, ciki har da guje-guje da tsalle tsalle da wasan iyo da kuma wasan dambe. Musamman ma guje-guje da tsalle tsalle, muna sa ran samun lambobin yabo a kan wasannin gudun dogon zango da marathon da kuma gudun mita 1000, wannan shi kuma burinmu a gun wasannin Olympics a wannan karo. Ina fatan 'yan wasan Tanzania za su bi Akhwari, su nuna kwarewarsu da karfin zuciyarsu, su zama jarumai, su cika burinsu."

Ba shakka, wasannin Olympics na tattare da mafarkin dimbin jama'a, shi ya sa babban taken wasannin Olympics na Beijing shi ne "duniya daya, mafarki daya." A game da taken, Akhwari ya ce, "kowa na da mafarkinsa, kuma kowa na fatan duniyarmu za ta yi ta kyautatuwa. A gun wasannin Olympics, kowa na iya cika burinsa. Ina son nuna godiya ga aminai 'yan birnin Beijing, da fatan za ku cika burinku a gun wasannin Olympics na Beijing."

Amma kullum ba a rasa samun wahalhalu a kan hanyar cimma mafarki. A nan kasar Sin, kowa ya san Sang Lan, wata 'yar wasan lankwashe jiki ta kasar Sin. A gun wata gasar da aka yi a shekaru 10 da suka wuce, Sang Lan ta ji rauni mai tsanani, har ma ta zama ba ta ji tun kirjinta har zuwa kasa idan an taba ta. Amma duk da haka, Sang Lan ba ta yi kasa a gwiwa ba, a maimakon hakan dai, ta ci gaba da kokari, ta kara dukufa a kan wasannin motsa jiki, har ta zama wakiliyar tashar internet ta kwamitin wasannin Olympics na kasar Sin. Ta ce, "A ganina, abin da ya fi muhimmanci shi ne a sa hannu a ciki, wasannin Olympics babban mafarki ne ga kowane dan wasa. Bayan da na ji rauni, ban iya sake zuwa wajen wasanni ba, domin in cika burina kamar yadda sauran 'yan wasa suke yi. Amma a hakika, ina ganin kowa na iya cika wannan buri ta wata hanya daban, sabo da haka, yanzu ina ayyukan da ke shafar wasannin motsa jiki ko wasannin Olympics da kuma harkokin ji dadin al'umma."

Ba ma kawai 'yan wasa ba, kowa na cika burinsa ta hanyar sa hannu cikin wasannin Olympics. Jin Xiao, wata dalibar da ke karanta harshen Swahili a jami'ar koyon ilmin yada labarai ta kasar Sin, yanzu ta kasance wata mai aikin sa kai wajen wasannin Olympics. Sabo da harshen da take koyo, shi ya sa ta san labarin Akhwari sosai. Ta ce, "A gare ni, abin da Akhwari ya yi a wajen gasa shi ne abin da nake bukata a zaman rayuwata. Ina ganin mutanen da ke da karfin daukar nauyi ya kamata ya yi iyakacin kokarin kammala duk abin da ke gabansa. Game da wasannin Olympics, kowa na da mafarkinsa, kada a yi sako-sako da shi, musamman ma lokacin da ake fuskantar matsaloli, kamata ya yi a tsaya tsayin daka a kansa. Burina shi ne in kammala aikin da ke bisa wuyata, in yi iyakacin kokarin gudanar da aikin sa kai kamar yadda ya kamata."

A game da manufar wasannin Olympics, Akhwari yana ganin cewa, "yawancin 'yan wasa ba za su iya zama na farko ko na biyu ba, amma abin da ya fi muhimmanci a cikin manufar wasannin Olympics shi ne a sa hannu a ciki, wato idan kana da karfin zuci wajen samun nasara, to, tabbas ne za ka samu nasara, amma idan ka yi kasa a gwiwa, to, ko shakka babu, ba za ka zama jarumi ba."

Kamar yadda Akhwari ya gaya mana, manufar wasannin Olympics shi ne kowa ya sa hannu a ciki, kowa na iya cika burinsa, kuma kowa na iya zama jarumi.(Lubabatu)