A ran 31 ga watan Yuli a nan birnin Beijing, Mr. Yang Guoqing, mataimakin shugaban hukumar zirga-zirgar jiragen saman fasinja ta kasar Sin ya bayyana cewa, hukumarsa za ta rubanya kokari domin samun tabbaci ga ayyukan hidima da take yi ga wasannin Olimpic.
A gun wani taron manema labaru da aka yi a wannan rana, Mr. Yang ya ce, daga ran 1 ga watan Agusta, kungiyoyin wakilan wasannin motsa jiki da 'yan kallo na kasashe daban-daban za su iso nan birnin Beijing. An kimanta cewa, yawan jiragen sama da za su tashi kuma za su sauka a filin jirgin sama na hedkwar kasa zai kai wajen 1,500 a kowace rana, wato zai karu da kashi 20 cikin 100 bisa na yau da kullum. Yawan fasinjojin da za su tashi ko kuma za su sauka a wannan filin jirgin sama zai kai wajen mutane dubu 260 a kowace rana, wato zai karu da kashi 25 cikin 100 bisa na yau da kullum. (Umaru)
|