Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-31 21:09:21    
Filayen wasannin Olympics na amfani da fasahohin zamani

cri
Gaba daya ne aka gina sabbin filayen wasanni 12 a nan birnin Beijing domin wasannin Olympics na karo na 29, kuma an nuna dimbin fasahohin zamani wajen gina wadannan filaye, wadanda suka bayyana mana manufar "wasannin Olympics da ke da fasahohin zamani".

Filin wasan kwale-kwale na Olympics yana arewa masu gabashin birnin Beijing, kuma ya kasance mafi fadi daga cikin sabbin filayen wasa da aka gina, har ma fadin ruwan da ke cikin filin ya kai muraba'in mita dubu 640. Mr.Li Dan, babban mai zane filin ya ce, filin ya kasance filin wasan kwale-kwale daya kurum a duniya wanda ya hada filin wasan kwale-kwale da ruwa ba ya gudana da kuma filin wasan kwale-kwale da ruwa ke gudana a gu daya. Ya ce, "Kafin mu zane filin, mun yi nazari sosai a kan yadda ake gudanar da wasannin Olympics a da. A gun wasannin Olympics na da, kusan duka an raba filin ruwan da ba ya gudana da kuma filin ruwan da ke gudana. Amma wannan filin wasan ya hada filayen biyu gu daya, ta yadda za a iya gudanar da shi bayan wasan kamar yadda ya kamata."

An ce, za a gudanar da gasannin wasan kwale kwale da iyon marathon da kuma wasan kwale-kwale na Olympics na nakasassu a wannan filin wasan, inda za a fitar da lambobin zinari 32, wadanda za su dau kimanin kashi 1/10 na lambobin zinari gaba daya da za a bayar.

A gun gasar gwaje-gwaje ta "Good Luck Beijing" da aka gudanar kwanan baya, filin wasan kwale-kwale na Olympics ya burge 'yan wasan gida da na waje kwarai da gaske, 'yan wasan kasar Sin ma sun nuna yabo sosai ga filin. Sun ce, "Hanyoyin ruwa a nan filin sun zama mafi kyau a duniya."

"Hanyoyin ruwa na da kyau sosai, kuma muhallin kewayen filin da kuma na'urorinsa suna da kyau sosai, filin ya cancanci yabo ko a gida ko kuma a waje."

A lokacin da ake gina filayen wasannin Olympics, an mai da hankali sosai a kan yin amfani da sabbin kayayyaki da fasahohi, don neman kiyaye muhalli da tsimin makamashi. Misali, wannan filin wasan kwale-kwale na Olympics ya yi amfani da tsarin musamman na kulawa da ruwa, wanda ya iya tabbatar da rashin fitar da gurbataccen ruwa.

Gidan wasan harbe-harbe da ke yammacin birnin Beijing zai dauki nauyin gudanar da gasannin harbe-harbe 10 a lokacin wasannin Olympics da kuma wasannin Olympics na nakassu. Inda wannan gidan wasa ya sha bamban da saura shi ne ya kasance rabi bude kuma rabi rufe, wato 'yan wasa suna cikin daki, a yayin da abin da ake hari yake waje. Mr.Qi Bin, wanda ya zana wannan gidan wasa ya ce,"Gidan wasan harbe-harbe ya kasance rabi bude kuma rabi rufe. Don yin la'akari da tsimin makamashi, mun kafa wani bango na canza iska, kuma mun zana ginin gaba daya da ya kasance tamkar ana farauta a cikin daji."

A hakika, bangon canza iska da Mr.Qi Bin ya ambata a baya wata fasahar zamani ce wajen tsimin makamashi, wanda zai iya canza iska mai sanyi da kuma iska mai zafi da iskar da ke cikin daki, bisa sauyin zafin iskar da ke cikin daki. Wato ke nan, ko ba a yi amfani da air-conditioner ba, 'yan wasa da ke saye da rigunan wasa masu kauri ba za su ji zafi ba.

An yi amfani da fasahohin zamani sosai wajen gina filayen wasanni na Olympics, ban da filayen wasa biyu da muka ambata a baya, akwai kuma shekar tsuntsu da water cube da dai sauransu. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, bi da bi ne Sin ta zuba kudin Sin kusan yuan biliyan 10, wajen nazarin fasahohi da kimiyyar da ke shafar wasannin Olympics, musamman ma a fannin gina filayen wasanni.(Lubabatu)