A ran 31 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Zhao Zilin, shugaban hukumar tsara shirin kudi ta ma'aikata kiwon lafiya ta kasar Sin ya ce, yawan kudin da za a ware domin farfado da tsarin kiwon lafiya wanda ya lalace sabo da mummuan bala'in girgizar kasa ya kai kudin Sin wajen Yuan biliyan 12, za a yi amfani da wadannan kudade ne musamman domin sake gina da yin gyare- gyaren dakuna, da sayen kayayyaki da na'urorin hukumar kiwon lafiya.
Bisa shirin da kasar Sin ta tsayar an ce, za a farfado da tsarin kiwon lafiya a gundumoni da birane da jihohi 51 da ke larduna 3 wato Sichuan da Shanxi da Gansu wadanda suka sha mummunan bala'in girgizar kasa, musamman ma ga hukumomin likitanci da kiwon lafiya na matakai daban-daban dake wadannan wurare.
An ce, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta roki kwararrun da abin ya shafa da su tsai da sunayen kayayyaki da na'urori iri 68 da za a saya domin asibitoci da dakunan kiwon lafiyar mata da yara na gundumomi da garuruwa daban-daban, ciki har da injin duba yanayin zuciya wato injin cardiogram da motocin asibiti, jimlar kudin da za a ware domin sayen wadannan kayayyaki ya kai wajen Yuan biliya 2. (Umaru)
|