Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-31 17:15:14    
Shugaban kasar Niger ya yi ban kwana da kungiyar wakilan 'yan wasan motsa jiki ta Olimpic ta kasar

cri
A ran 30 ga watan Yuli a birnin Niamey, hedkwatar kasar Niger, shugaba Mamadou Tandja na kasar ya gana da kungiyar wakilan 'yan wasan motsa jiki ta Olimpic ta kasar kuma ya yi ban kwana da ita kafin ta tashi zuwa nan birnin Beijing domin halartar wasannin Olimpic.

Mr. Tandja ya yaba wa 'yan wasan sabo da su ne masu nuna biyayya ne ga dokoki kuma masu karfin zuciya, kuma yana fatan za su samu nasara a gun wasannin Olimpic.

Kungiyar wakilan kasar Niger tana hade da mutane fiye da 30, ciki har da 'yan wasa 5 wadanda za su shiga gasannin guje-guje da tsalle-tsalle da iyo da kuma wasan karate. Kungiyar kuma za ta tashi daga Niger a ran 1 ga watan Agusta kuma ta zo nan birnin Beijing ne don halartar wasannin Olimpic. (Umaru)