Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-31 16:02:04    
Muna begen more al'adun gargajiya na kasar Sin, a cewar shugaban kungiyar 'yan wasannin Olympics ta kasar Benin

cri
A ran 29 ga wata, an yi iska mai dadi da kuma ruwan sama kadan a birnin Beijing. Da karfe 11 ga wata na safe, an shirya bikin daga tuta don kungiyar 'yan wasannin Olympics ta kasar Benin a kauyen 'yan wasannin Olympics na Beijing.

Jamhuriyar kasar Benin tana yammacin Afirka, yawan mutanenta ya kai fiye da miliyan shida, kuma ba ta nuna gwaninta a fannin wasannin motsa jiki ba. Amma 'yan kasar suna nuna kauna sosai ga wasannin motsa jiki da kuma wasannin Olympics. An kafa kasar Benin a shekara ta 1960, kuma bayan shekaru biyu, ta shiga kwamitin wasannin Olympics na duniya, haka kuma daga shekara ta 1972 har zuwa yanzu, ta riga ta shiga wasannin Olympics har sau 8 gaba daya. Charles Nobre, shugaban kungiyar 'yan wasa ta kasar Benin ya taba shiga wasannin Olympics har sau 7. Kuma ya bayyana cewa,

"A idona, ban da samun lambobin zinariya da kuma cimma nasara, gasar wasannin Olympics wani gagarumin biki ne da ke iya nuna babbar jituwa a tsakanin 'yan Adam, inda a kan dora muhimmanci kan ra'ayin sa hannu a ciki. Ina fatan gasar wasannin Olympics za ta iya kawo wa kasashe da shiyyoyi daban daban zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta yadda jama'ar duniya za su hada kansu don zama 'yan uwa."

Mr. Charles Nobre ya fahimci ajanda da kuma tsarin shirya wasannin Olympics sosai. Kuma bayan kwanaki da dama da kungiyar 'yan wasa ta kasar Benin ta shiga kauyen 'yan wasannin Olympics, ayyukan share fagen gasar sun shaku cikin zuciyarsa sosai. Kuma ya bayyana cewa,

"Ko abinci mai dadin ci, ko zirga-zirga mai kyau, ko maraba da aka nuna wa kungiyoyin 'yan wasa da hannu biyu biyu, dukkansu sun sanya mu gano cewa, tabbas ne gasar wasannin Olympics ta Beijing za ta samu nasara sosai."

Bisa labarin da wakilinmu ya samu, an ce, domin ba da hidima sosai a fannin abinci a lokacin gasar wasannin Olympics, kwamitin shirya gasar na Beijing ya tattara masu dafa abinci da masu ba da hidima fiye da 2400 daga wurare daban daban na duk duniya domin samar da abinci mai dadi har sa'o'i 24 a ko wace rana a kauyen 'yan wasannin Olympics. Ban da abincin duniya da na Judah da na musulmi da kuma na Indiya, za a samar da abinci na Asiya da yawansu ya kai sulusi a cikin dukkan abinci da za a samar a kauyen. To, ko 'yan wasa na yammacin Afirka suna iya dacewa da irin wannan abinci? Mr. Charles Nobre ya gaya mana cewa,

"Kauyen 'yan wasannin Olympics ya bayar da hidima sosai wajen abinci, kuma abincin yana da dadi kwarai. Na yi imanin cewa, dukkan 'yan wasa na kasarmu suna masu sha'awar abincin sosai. Na taba zuwa shiyyar HongKong ta kasar Sin da kasashen Singapore da Cambodia da sauran kasashen Asiya, kuma na san abincin Asiya sosai."

Kasar Sin wata kasa ce da ke da dogon tarihi da al'adun gargajiya a gabashin duniya. Amma game da 'yan Afirka, kasar Sin cike take da asiri sosai. Shi ya sa 'yan wasa na kasar Benin suna son kara fahimtar kasar Sin a wannan karo. Charles Nobre ya gaya mana cewa,

"Na yi imanin cewa, tabbas ne za mu more al'adun al'ummar Sin sosai a gun bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing, muna farin ciki muna iya kara fahimtar al'adun kasar Sin ta wannan gagarumin bikin."(Kande Gao)