Kwanan nan an yi ruwa sau 2 bi da bi a nan birnin Beijing, shi ya sa iskar birnin yana da tsabta. A ran 30 ga wata, matsakaicin yawan ma'aunin gurbatar iska da tashoshi 27 masu duba ingancin iska na birnin suka bincika ya kai 44, wato ingancin iska ya kai mataki mafi kyau.
An ce, daga cikin tashoshi 27 masu duba ingancin iska na birnin Beijing, da akwai 18 ciki har da cibiyar wasannin motsa jiki ta Olimpic dake unguwar Chaoyang, wadanda matsakaicin yawan ma'aunin gurbatar iska da suka binciko bai kai 50 ba, wato ingancin iska na wadannan wurare ya kai mataki mafi kyau, sauran wurare kuma sun kai mataki na 2 wato suna da dan kyau, muhimman abubuwan kazanta na wadannan wurare dukkansu kananan kwayoyin da ake iya shaka ne. (Umaru)
|