Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-30 21:47:58    
Kasar Sin tana rubanyan kokari domin tabbatar da ingancin abinci a gun wasannin Olimpic

cri
A ran 30 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Ji Zhengkun, jami'in babbar hukumar sa ido kan ingancin kayayyakin kasar Sin ya bayyana cewa, hukumarsa tana rubanyan kokari domin tabbatar da ingancin abinci a gun wasannin Olimpic.

Mr. Ji ya bayyana cewa, ya kasance da masana'antu 214 wadanda ke yin abinci domin wasannin Olimpic, hukumar sa ido kan ingancin kayayyaki ta riga ta dauki kwararan matakai da yawa domin kara sa ido kan ingancin abincin da wadannan masana'natu suka fitar, ya ce,

"Mataki na farko da aka dauka shi ne, za a aike da injiniyoyi zuwa wadannan masana'antu domin sa ido ga aikinsu cikin awoyi 24 na kowace rana. Na 2, A sa ido kan danyun kayayykin da ake amfani da su wajen yin abinci. Na 3, A sa ido kan abincin da aka fitar daga wadannan masana'antu, duk irin abincin da su kai ma'aunin da aka tsayar wajen inganci ba, za a hana su fita daga masana'antu. Na 4, an yi tsare-tsare cikin nitsuwa wajen samar da abinci ga wuraren wasannin Olimpic." (Umaru)