Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-30 20:13:57    
An mai da hankali wajen kiyaye kayayyakin tarihi lokacin da ake gina filaye da dakunan wasannin Olimpic na Beijing

cri
A ran 30 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Kong Fanshi, shugaban hukumar kayayyakin tarihi ta birnin Beijing ya bayyana cewa, birnin Beijing yana mai da hankali wajen kiyaye kayayyakin tarihi lokacin da ake gina filaye da dakunan wasannin Olimpic, alal misali, lokacin da ake gina wurin wasan da ake kira "Water Cube" wato cibiyar wasan iyo ta kasa, an gusar da wurin ginawar zuwa arewa misali da mita 100 domin kiyaye wani wurin kayayykin tarihi.

A gun wani taron manema labarun da aka yi a wannan rana a nan birnin Beijing, Mr. Kong ya bayyana cewa, a lokacin da birnin Beijing yake gina filaye da dakunan wasannin Olimpic, yakan kiyaye kayayyakin tarihi da ke kan kasa ko a karkashin kasa ta hanyar tsara fasali da kuma yin bincike, kuma ya tono kayayyakin tarihi a wurare 18 da ake gina filaye da dakunan wasannin Olimpic. Ban da wannan kuma, birnin Beijing ya tsamo fasaha da tunani masu ci gaba da aka samu a wasu kasashen Turai wajen kiyaye shahararren birni mai dogon tarihi, kuma an gayyaci kwararrun kasar Faransa da na Jamus don su shiga ayyukan kiyaye da kuma kyautata wasu ni'imomin wuraren ban sha'awa na tarihi da ke nan birnin Beijing. (Umaru)