Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-30 19:40:09    
A idanun jama'ar da suka zo daga kasashen waje, birnin Beijing ya cika alkawarin da ya yi a yayin da ake neman shirya gasar wasannin Olympics

cri

Kafin shekaru 7 da suka gabata, hukumar wasannin Olympics ta duniya ta amince da alkawari da aniyar kasar Sin, ta mayar da ikon shirya gasar wasannin Olympics ta shekarar 2008 a hannun birnin Beijing. A halin yanzu dai, za a shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing a nan gaba ba da dadewa ba, ko birnin Beijing ya cika alkawarinsa a fannonin tsara fasalin birnin, da kare muhalli, da kuma ba da hidima mai kyau ga manema labaru ko a'a ? Bayan da jami'ai da manema labaru da suka zo daga kasa da kasa suka yi rangadi a birnin Beijing, suna ganin cewa, birnin Beijing ya riga ya cika alkawarinsa a fannoni daban daban, suna cike da imani cewa, birnin Beijin zai ci nasara wajen shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Jami'in hukumar wasannin Olympics ta duniya Mr. Alex Gilady ya yaba wa fasahohin zamani da aka yi amfani da su wajen gina dakin 'water cube' mai siffar 'tafkin wanka'. Ya ce,

'Kome yana da kyau sosai. Abun da ya fi muhimmanci shi ne, 'yan wasa suna iya iyo cikin sauri, mai yiyuwa ne za su karya matsayin bajinmta na tarihi.'


1 2 3