Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-29 20:54:39    
Biranen da ke hada gwiwa da birnin Beijing wajen gudanar da wasannin Olympics a shirye suke

cri

A gabannin wasannin Olympics na Beijing, biranen Shanghai da Tianjin da Shenyang da Qingdao da Qinhuangdao da kuma Hongkong, wadanda za su hada gwiwa da Beijing wajen gudanar da wasannin sun riga sun shirya sosai da sosai.

Birnin Shanghai ya share fage sosai domin gasar wasan kwallon kafa ta Olympics da za a yi a birnin. Tun daga karshen watan Mayu, filin wasan da ke iya daukar mutane dubu 80 ya fara share fagen gasar, kuma masana sama da 10 sun shafe shekara fiye da daya suna kulawa da ciyayin da aka dasa a kan filin. Domin tabbatar da tsaro a wajen wasannin Olympics, kwanan baya, birnin Shanghai ya kuma gudanar da rawar daji ta musamman don yaki da ta'addanci. Ban da wannan, an kuma sanya alamun da ke da rubutun Sinanci da Turanci a muhimman wurare na birnin Shanghai. Mr.Han Zheng, magajin garin birnin Shanghai ya ce, alamun za su iya samar wa mutanen kasashen waje sauki lokacin da suke birnin Shanghai don kallon wasannin Olympics. Ya ce, "kullum muna nanata cewa, kada a mayar da rubutun Sinanci ya zama girma, a yayin da a mayar da rubutun Turanci ya zama karami, wato muna son kowa na iya gane shi cikin sauki."

A matsayinsa na birnin da ya fi kusa da birnin Beijing, birnin Tianjing na share fagen wasannin Olympics kamar yadda ya kamata. Abin da ya fi jawo hankulan jama'a a birnin Tianjin shi ne sufuri da kuma filin wasa. A ran 1 ga watan Agusta, za a fara aiki da wata hanyar dogo mai saurin gaske a tsakanin biranen Beijng da Tianjin, wadda ke iya gudu da kilomita 300 a kowace awa, wato cikin minti 30 ne kawai za a iya isa birnin Tianjin daga Beijing. Sa'an filin wasan Olympics da ke birnin Tianjin, wanda ake kiransa "digon ruwa", yana iya daukar masu kallo kusan dubu 60, kuma ya kware sosai a wajen na'urorinsa.

Sai kuma a birnin Shenyang, wanda zai hada gwiwarsa da birnin Beijing wajen gudanar da gasar kwallon kafa, an fara gina babban filin wasan Olympics da ake kiransa "Crystal Crown" yau da shekaru biyu da suka wuce, kuma an kammala shi a shekarar bara tare da samun babban yabo daga shugabannin kwamitin wasannin Olympics na Beijing. Ban da wannan, 'yan birnin Shenyang suna matukar zakuwa kan wasannin Olympics da za a soma yi ba da jimawa ba. Mr.Xu Dadi. shugaban ofishin kula da harkokin wasannin Olympics a birnin Shenyang, ya ce, "Shenyang birni ne mai al'ajabi, shi ne wurin da ake kirkiro mafarki. Mutanen birnin Shenyang suna da jaruntaka a cikin jininsu, kuma suna mai da hankula na musamman a kan gasar kwallon kafa da za a gudanar a nan birnin."

Qingdao wani kyakkyawan birni ne da ke bakin teku, kuma zai gudanar da gasanni 9 a lokacin wasannin Olympics, ciki har da tseren kwale-kwale da kananan kwale-kwale, inda za a fitar da lambobin zinari 11. Madam Zang Aimin, mataimakiyar magajin garin birnin ta ce, birnin Qingdao a shirye yake."Muna da imani sosai, kuma Qingdao a shirye yake. Ko da yake yanzu muna fuskantar kalubalen daga kainuwa, amma bisa kokarin da muka yi, mun samu wasu nasarori. Sabo da haka, a ganina, muddin muka bi yadda kwamitin wasannin Olympics ke bukata, mu yi iyakacin kokarinmu da kuma yin amfani da basirarmu, to, kome zai gudana kamar yadda aka tsara."

A lokacin da ake kidayar kwanakin da za a bude wasannin Olympics, biranen Qinhuangdao da Hongkong su ma sun share fage sosai, suna sa rai ga wasannin Olympics.(Lubabatu)