Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-29 16:11:08    
'Yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Kenya suna kara gaggautawar shiga horon da aka yi musu don tinkarar samun lambawan a wasannin Olimpic na Beijing

cri
A gun wasannin Olimpic da za a yi a birnin Bejing, kasar Kenyar da ke da karfi sosai wajen gasannin wasannin guje-guje da tsalle-tsalle a gabashin Afrika za ta turo 'yan wasanta su 37 don shiga gasannin gajeran guje-guje da dogayen guje-guje da wasan tseren gudu da dunduniya na kilomita 20 da gudun famfalaki wato Marathon da gasar gudun da aka yi tare da tsallake shinge da sauransu don neman samun lambobin zinariya. Yanzu yaya wadannan 'yan wasan suke yin horonsu? Wane irin babban kalubale  za su fuskanta? Yaya za su magance shi? Yanzu ga labarin da wakilan gidan rediyon kasar Sin ya ruwaito mana daga birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya.

Birnin Kasarani da ke arewancin birnin Nairobi shi ne sansanin horar da 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Kenya. A lokacin da bai kai karfe 8 a safiya, Mr Richard Kipkemboi mai shekaru 24 da haihuwa wanda ya zama dan takarar wasan guje-guje na mita dubu 3 tare da tsalleke shinge ya soma shiga horonsa na yini daya. Don samun sakamako mai kyau, a kowace rana, Mr Richard yana bukatar yin tsalle-tsalle har sau dubu ko fiye don kara karfinsa wajen wasan tsalle-tsalle. Lokacin da ya tabo magana a kan wasannin Olimpic na Beijing, Mr Richard ya yi farin ciki sosai da cewa, na soma rayuwata ta yin wasan motsa jiki ne a shekarar 2004, a wancan shekarar, na taba shiga gasar fitar da gwanni domin wasannin Olimpic na Athens. Amma, sakamakon da na samu bai kai matsayi mai kyau ba, na kai matsayi na biyar kawai, shi ya sa ban sami damar shiga wasannin Olimpic na Athens ba, amma ban yi kasala ba, daga wancan lokaci, ina kara kokarin horar da ni kaina, bayan kokarin da na yi cikin wasu shekarun da suka wuce, sai na sami ci gaba sosai. A shekarar da muke ciki, a karshe ne na sami damar shiga wasannin Olimpic na Beijing. Na yi kokari sosai, ina fatan zan kara samun ci gaba, duk saboda samun lambar zinariya a wasannin Olimpic mafarkina ne.

Halin da Mr Richard ke ciki na da kyau sosai a shekarar da muke ciki, a wata gasar da aka shirya a Afrika kafin wasu watannin da suka wuce, Mr Richard ya ci lambawan, ya kara alfahari ga kasarsa ta mahaifa.

Wani dan wasa daban, wato dan wasa mai shekaru 22 da haihuwa Mr Edwin Cheruiyot Soi zai halarci gasar gudu na mita dubu 5 da na dubu goma a wasannin Olimpic na Beijing, a gun gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da aka yi a shekarar bara, shi kansa ya samu dukkan lambobin zinariya na mita dubu 3 da na dubu goma. Kodayake sakamakon da ya samu mai kyau ne, amma Mr Edwin bai yi kasala ba, ya bayyana cewa, yanzu babban matsin da ke gare ni shi ne wasu manyan kasashen da ke da karfin takara wajen gasar guje-guje da tsalle-tsalle, alal misali, kasar Habasha da kasar Amurka. Matsayin 'yan wasan kasashensu ya kai na daya ko na biyu. Ina fatan Allah zai taimake mu wajen cim ma burinmu na samun lambobin zinariya.

Amma Mr Edwin ya kuma bayyana cewa, da zuciya daya ne nake fatan zan cim ma mafarkina na samun lambar zinariya a wasannin Olimpic na Beijing, duk saboda tun daga farkon lokacin da na soma rayuwata ta yin wasan motsa jiki, na yi kokari sosai, a cikin shekaru da yawa, ban taba kasala ba wajen horar da ni wajen motsa jiki.

Wajen 'yan wasan kasar Kenya, babban kalubalen da za a kawo musu shi ne yanayin sararin samaniya na Beijing. Kasar Kenya tana kusa da Ekwatar duniya, tana Palatau na gabashin Afrika, yanayin sararin samaniya na kasar yana da dan zafin kawai, amma birnin Bejing yana kasancewa a yanayin zafi, shi ya sa akwai zafi sosai. Saboda haka 'yan wasan kasar Kenya za su gamu da wahalhalu da yawa, yanzu suna kokarin dacewa da yanayin birnin Beijing.

Mun sami labari cewa, kasar Kenya za ta tura 'yan wasa da yawansu ya kai 49 don halartar wasannin Olimpic na Beijing, ban da 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsaclle da yawansu ya kai 37,sai da akwai 'yan wasan dambe biyar tare da wasan tae-kwodo biyu da wani dan wasan tsallen kwale-wale. (Halima)