Assalamu Alaikum, barkanku da war haka, barkanmu da saduwa da ku a wannan sabon shirimu na "biranen da suka taba daukar nauyin gudanar da wasannin Olympics". Ni ce Kande ke gabatar muku da wannan shiri. A shekara ta 1968, an shirya gasar wasannin Olympics ta karo na 19 cikin nasara a birnin Mexico City, babban birnin kasar Mexico, kuma an gina wani kauye don 'yan wasannin Olympics. Daga baya kuma kauyen 'yan wasannin Olympics ya zama filin motsa jiki na dimbin 'yan kasar Mexico da kuma dakunan kwana na aji na farko a wurin. Ba kawai gine-ginen da ke cikin kauyen suna da kyakkyawan salo ba, har ma suna da inganci sosai, wadanda suka taba fama da girgizar kasa mai karfin digiri 7.8 bisa ma'aunin Richter da ta auku a kasar a shekara ta 1985 cikin nasara. To yanzu ga cikakken bayani.
"An gina kauyen 'yan wasannin Olympics ne domin warware matsalar cin abinci da yin barci da 'yan wasa na kasashe daban daban da suka shiga gasar wasannin Olympics ta Mexico City ta shekara ta 1968 ke tinkarar. Haka kuma kasar Mexico ta zama kasa ce ta farko a wancan lokaci wajen sayar da dakunan da ke cikin kauyen bayan gasar wasannin Olympics domin fararen hula suna iya zama a ciki. Dimbin 'yan kasar sun sayi dakanan, kuma har yanzu suna zama a ciki. Sabo da haka ana iya samun mutane masu yawa da suka dade suna zama a cikin kauyen har shekaru 40. Yanzu halin da kauyen ke ciki yana da matukar kyau, muhallinsa na da kyau, kuma ana iya samun manyan kantuna da bankuna da kuma dakunan cin abinci a kewayensa, shi ya sa ake nuna maraba sosai ga wannan unguwar dakuna ta aji na farko."
Abin da kuka saurara dazun nan bayani ne da Madam Nancy Badager, shugabar ofishin kula da ayyukan gudandar da kauyen 'yan wasannin Olympics na Mexico ya yi mana. Haka kuma bisa matsayinta na wata 'yar kauyen, tana kaunar wannan unguwa kwarai.
Ban da wannan kuma ana iya samun wani babban filin wasa a kusa da yankin dakunan kwana da ke cikin kauyen 'yan wasannin Olympics, ya zuwa yanzu ana yin amfani da wannan cibiyar wasa, wadda 'yan wasa na kasashe daban daban da suka shiga gasar wasannin Olympics ta karo na 19 suka taba yin horaswa a ciki. Mr. Mateo, mai kula da ayyukan cibiyar ya bayyana cewa, yanzu dukkan mazaunan birnin Mexico City suna iya motsa jiki da kuma yin harkokin nishadi a wurin. Kuma ya kara da cewa,
"Wannan ita ce wata cibiyar wasa ta jama'a, ana bukatar kashe kudade kadan wajen yin amfani da ita. Game da yaran da shekarunsu ya kai 6 zuwa 16 da haihuwa, muddin sun biya kudaden dala shida, to za su iya shiga kwasa-kwasan horaswa iri daban daban, kamar wasan karate da na ninkaya da na kokawa da guje-guje da kuma na salon-iyo. Haka kuma idan baligai suka biya kudade dala 15 a ko wane wata, to za su iya motsa jiki a wurin. Bisa dokokin kasar Mexico, dole ne gwamnatin birnin Mexico City ta samar da ayyukan ba da hidima ga nakasassu a fannin motsa jiki. Sabo da haka ne muka kafa cibiyar samun jiyya da kuma shirya kwasa-kwasan motsa jiki a wurin."
A 'yan shekarun nan da suka gabata, ana ta kyautata muhimman ayyukan yau da kullum na cibiyar wasa. Rodolfo Krieger, wani ma'aikaci na cibiyar ya gaya mana cewa,
"An yi amfani da wadancan alluna da ke kan gine-gine ne domin samun hasken rana, ta yadda za a iya dumama ruwan da ke cikin wurin ninkaya. Ana iya samun allunan samun hasken rana 52, wadanda suke iya dumama ruwa litre 7000. An gina su ne yau da shekaru 3 da suka gabata, yanzu ya kamata mu kaddamar da amfani da makamashi marasa gurbata muhalli."(Kande Gao)
|