Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-28 17:52:01    
Kasashen duniya suna maraba da zuwan wasannin Olimpic na Beijing tare

cri
A yayin da lokacin bude wasannin Olimpic na beijing ke kusantowa, ana nan ana yin bukukuwa da yawa da suka shafi wasannin Olimpic a kasashen duniya, mutane sun yi haka ne domin nuna kyakkyawan fatan alheri ga wasannin Olimpic na Beijing. To, jama'a masu sauraro yanzu za mu kawo muku wani bayani da wakilinmu ruwaito mana mai lakabin haka, Kasashen duniya suna maraba da zuwan wasannin Olimpic tare.

A ran 21 ga wata a hedkwatar MDD da ke birnin New York, an bude babban nuni mai suna "Duniya daya wato nunin hotunan da masu aikin zane-zane na kasar Sin suka zana dangane da babban iyalin MDD", wannan nuni ya dace da wasannin Olimpic na Beijing sosai. A wannan rana kuma Mr. Ban Ki-moon, babban sakataren MDD ya halarci bikin bude nuni kuma ya nuna kyakkyawan fatan alheri ga kasar Sin da ta samun nasara wajen shiryar wasannin Olimpic, ya ce, "Ayyukan da kasar Sin ta yi wajen shirya wasannin Olimpic sun ba ni zurfaffiyar alama a zuciyata, filaye da dakunan wasannin motsa jiki suna da kyau kwarai har ban taba ganin irin su ba a tarihi."

A ran 17 ga wata da dare na agogon wurin, a "Garin Dodo" da ke birnin Dubai na kasar Hadaddiyar daular Larabawa, an yi bikin fara ayyukan da kwamitin wasannin Olimpic na Hadaddiyar daular Larabawa da ofishin Consulate na kasar Sin da ke birnin Dubai suka shirya tare domin muraba da zuwan wasannin Olimpic na Beijing, wannan ya tasam ma wani babban matakin da Sinawan da ke hadaddiyar daular Larabawa da aminanmu na wannan kasa suka dauka domin maraba da zuwan wasannin Olimpic cikin farin ciki. Mr. Gao Youzhen, babban consulate na kasar Sin da ke birnin Dubai ya bayyana cewa, "A nan mu Sinawa masu nagarta da aminanmu da suka zo daga Hadaddiyar daular Larabawa da sauran kasashe mun taru gu daya domin yin maraba da zuwan wasannin Olimpic na Beijing tare, wannan ya shere mu kuma ya faranta mana rai sosai".

An yi wannan biki ne daga ran 17 zuwa ran 28 ga wata, a gun bikin 'yan wasan da suka zo daga kasar Sin za su nuna wasannin motsa jiki ciki har da wasan lankwashe jiki da wasan kwallon tebur da wasan karate da wasan Judo da sauran wasannin fasaha. Mr. Ibrahim Abdulmalek, babban sakataren kwamitin wasannin Olimpic na Hadaddiyar daular Larabawa ya yi farin ciki da cewa, "A gabannin bude gasar wasannin Olimpic ta Beijing, muna yin bukukuwan maraba da zuwa wannan gasar a Hadaddiyar daular Larabawa, makasudinmu shi ne domin bayyana burin jama'ar kasarmu wajen nuna goyon baya ga kokarin da da jama'ar kasar Sin yi domin shirya wasannin Olimpic."

Kwanan baya kasar Tailand wadda take da dangantakar zumunci ta gargajiya a tsakaninta da kasar Sin ita ma ta shirya bukukuwa da yawa domin maraba da zuwa wasannin Olimpic na Beijing. A ran 20 ga wata da dare a cibiyar al'adun kasar Tailand da ke birnin Bangkok, an nuna wasa mai sunan "Nuna kaunar-zuci ga wasannin Olimpic na Beijing.

Ban da wannan kuma, a kasar Japan an yi nunin hotuna mai sunan "Beijing yana nuna maka maraba". A kasar Argentina kuma an yi shirin bude bikin nuna wasanni a wurin ibadan da ke birnin Buenos Aires a ran 8 ga wata mai zuwa wato ranar bude wasannin Olimpic na Beijing.  (Umaru)