Gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta zama gasar da take da 'yan wasan badminton mafi yawa a tarihin gasannin Olympic. A cikin dukkan 'yan wasan da suka zo daga kasashe daban daban, a karo na farko ne za a ga 'yan wasan badminton na Afirka, kamar Grace Daniel, wata 'yar wasan ta kasar Najeriya, kuma ita 'yar wasan kadai da ta zo daga kasashen Afirka, za ta halarci gasar wasan badminton a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing.
Yarinya Grace Daniel tana da kyaun gani. A da, ba a taba samun wata 'yar wasa ta kasashen Afirka ba a gun gasar wasan badminton ta gasar wasannin Olympic. Yanzu Grace Daniel tana farin ciki sosai saboda za ta kama kan hanyar zuwa Beijing. Grace ta ce, "Na iya zama 'yar wasan badminton ta farko ta kasashen Afirka a gun gasar wasannin Oympic, ina jin alfahari sosai tare da annashuwa, wannan kuma abin alfahari ne a gare ni."
Haka ne, ya kamata Grace Daniel ta ji alfahari sabo da kanta. Ta riga ta yi namijin kokari wajen neman samun izinin halartar gasar wasannin Olympic. Yarinya Grace Daniel ta yi shekaru 2 tana horaswa a kasar Jamus domin neman izinin halartar gasar wasannin Olympic ta Beijing. A karkashin taimakawar nagartaccen mai koyarwa, ta samu cigaba sosai kan fasahohin wasan badminton. Ta ce, dalilin da ya sa ta rinka yin kokari ba tare da kasala ba shi ne tana son cimma burinta na halartar gasar wasannin Olympic.
"Na sha wahala sosai lokacin da nake horaswa, bayan da na yi namijin kokari kamar haka, na sami izinin halartar gasar wasannin Olympic. Daliliin da ya sa na yi haka shi ne ina son cimma burina na halartar gasar wasannin Olympic. Halartar gasar Olympic, kuma fahimtar gasar da kaina wani buri ne da na dade ina son cimmawa."
Yanzu, yarinya Grace Daniel za ta iya cimma burinta na halartar gasar Olympic a Beijing. A matsayin kasar da ke da karfi sosai a fannin wasan badminton, kasar Sin kasa ce da yarinya Grace Daniel take girmamawa. A idonta, kasar Sin suna ne da ke wakiltar wasan badminton. Halartar gasar wasan badminton a kasar Sin tana da ma'ana daban. Wannan zakarar Afirka tana cike da imani sosai ga gasar da za a yi a tsakaninta da sauran nagartattun 'yan wasan badminton. Yarinya Grace ta ce, "A gare ni, kasar Sin garin wasan badminton ne. Na sani, akwai nagartattun 'yan wasan badminton masu dimbin yawa a kasar Sin. Amma tabbas ne zan yi kokarina. Na riga na tsai da kudurin halartar gasar wasannin Olympic, ba zan kula da wane ne zai yi gasa da ni ba, ina son yin kokarina a gun gasar, kuma ina fatan duk nahiyar Afirka za ta ji alfahari sabo da ni."
Ban da gasar da za ta halarta, yarinya Grace Daniel tana ganin cewa, wannan ziyararta a gun gasar Olympic za ta kawo mata dimbin abubuwan da take bukata. "Sabo da za ka iya sanin dimbin mutane da al'adu iri daban daban kuma da hanyoyin zaman rayuwa iri iri. Sabo da haka, wannan ba wata gasar wasannin motsa jiki kawai ba, a gun gasar Olympic, za mu iya tuntubar juna, kuma za mu iya koyon dimbin abubuwa iri daban daban."
A ran 26 ga watan Yuli da muke ciki, an riga an bayar da ajandar yin gasar wasan badminton na mata. A gun zagaye na farko, Grace Daniel za ta yi gasa da Kristina Ludikova ta kasar Czech. Idan za ta iya cin nasara a gun wannan gasa, sannan za ta yi gasa da Ye Peiyan, wata 'yar wasan badminton ta Hongkong wadda take matsayi na 12 a duk duniya. Sabo da haka, wannan gasa za ta zama wata gasa mai tsanani a gare Grace Daniel. Amma Grace Daniel ta riga ta samu girmamawa daga kasashen duniya sabo da za ta iya halartar gasar Olympic a madadin kasashen Afirka. Muna fatan Allah Ya kiyaye wannan yarinya ta kasar Najeriya a gun gasar Olympic ta Beijing. (Sanusi Chen)
|