Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-28 15:06:40    
Bari mu yi kokari tare domin cimma burinmu daya, a cewar jakadan kasar Bangladesh da ke nan kasar Sin

cri

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na "Gasar Olympic ta Beijing a idon jakadun kasashen duniya da ke nan kasar Sin". Ni Sanusi Chen ne zan ja akalar wannan shiri. A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku wata hirar da aka yi a tsakanin wakilinmu da Munshi Faiz Ahmad, jakadan kasar Bangladesh da ke nan kasar Sin.

Munshi Faiz Ahmad jakadan kasar Bangladesh da ke nan kasar Sin yana da sha'awa sosai kan wasannin motsa jiki. Ya ce, ya fi son kallon shirye-shiryen wasannin motsa jiki. Idan babu aiki, yana iya kallon shirye-shiryen wasannin motsa jiki a gaban talibijin har yini daya. Sabo da haka, yana farin ciki sosai sabo da zai iya kallon gasar wasannin Olympic ta Beijing a wannan karo. Mr. Munshi ya ce, "Gasar wasannin Olympic tana kasancewa a gabana tamkar wani mafarki. Na taba kallo da kuma karanta labarun gasar wasannin Olympic a talibijin da jaridu, amma ba a taba shirya gasar a kasashen da ke makwabtaka da kasar Bangladesh ba. A wannan lokaci, za a shirya gasar wasannin Olympic a kasar Sin, kuma lokacin da ake gasar, ina nan kasar Sin. Sabo da haka, gasar wasannin Olympic tana kasancewa a gabana tamkar wani mafarki. Yanzu zan cimma wannan burina, ina jiranta cike da anashuwa."

Mr. Munshi ya ce, kamar yadda sauran mutanen kasar Bangladesh suke ciki, yana kuma farin ciki sosai lokacin da yake kallon gasannin wasannin motsa jiki. A gun wata gasar, wasu iyalansa suna goyon bayan wani bangare, amma sauransu mai yiyuwa ne suna goyon bayan bangare daban, suna sa kaimi ga bangaren da suke so. Amma daga karshe dai, kowane bangare ya samu nasara, dukkan iyalansu suna farin ciki suna ihu tare. Mr. Munshi ya nuna cewa, wannan shi ne karfin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics, wato karfi ne da ke hada kan dukkan mutane.

"Kamar gasar wasannin Olympic ta Beijing take kira, 'ana da mafarki daya a duniya daya'". Dukkan 'yan Adam kabila daya ne, dukkanmu muna da mafarki daya. Muna bukatar dukkan 'yan Adam na duniyarmu da su hada kan juna domin fuskantar matsalolin da ke kasancewa a gabanmu, da kuma neman hanyar warware su tare. Sabo da haka, ina ganin cewa, gasar wasannin Olympic wani kyakkyawan kuma kasaitaccen al'amari ne da ke bayyana wani karin maganar Sinawa, wato 'dukkan mutanen da suke da zama a yankuna daban daban na duniya 'yan uwa ne'".

Mr. Munshi ya ce, har yanzu bai samu damar kai ziyara ga muhimman dakuna da filayen wasannin motsa jikin na gasar wasannin Olympic ta Beijing ba, amma matarsa da matan sauran jakadun kasashen waje da ke nan kasar Sin da wasu jakadu mata na kasashen waje da ke nan kasar Sin sun riga kai ziyara ga wadannan dakuna da filayen wasannin Olympic bisa gayyatar da gwamnatin birnin Beijing ta yi musu. Sabo da haka, Mr. Munshi yana fatan gwamnatin birnin Beijing za ta gayyaci jakadu maza da su kai ziyara ga wadannan dakuna da filayen wasannin motsa jiki na Olympic.

Mr. Munshi ya fi son wasannin Pinpon da Badminton. Lokacin da yake koyon harshen Sinanci a nan Beijing a tsakanin shekarar 1981 da 1983, ya kan yi wasa da Pinpon da abokan ajinsa. Amma Mr. Munshi ya yi tsammani cewa, tun daga yake karami ne ya soma yin sha'awar wasan Pinpon. "Tun daga nake karami, na yi sha'war wasan Pinpon sosai. Ko da yake ban iya wasa da shi da kyau ba, amma ina da sha'awar wannan wasa kwarai. Kanena ya koyi fasahar wasan Pinpon da ni. Daga baya, ya zama zakarar wasan Pinpon a kasar Bangladesh."

Kazalika kuma, Mr. Munshi ya ce, ya san 'yan wasan kasar Sin sosai. "Kasar Sin tana da 'yan wasa da yawa da nake so. Amma abin bakin ciki shi ne ban iya tunawa da dukkan sunayensu ba. Na haddace sunan 'yar wasan Pinpon Wang Nan, da 'yar wasan lankwashe jiki Liu Xuan. Ko da yake ban iya haddace dukkan sunayensu ba, amma na kan zura ido kan gasanninsu. Ina fatan za su kara samun sakamako mai kyau."

Game da wasannin motsa jiki da 'yan kasar Bangladeshi suke gwaninta, Mr. Munshi ya ce, kasar Bangladeshi tana samun cigaban wasannin motsa jiki. Wasannin motsa jiki da suka fi gwaninta su ne wasan kurket da wasan harbi da na guje-guje. Amma har yanzu ba ta samu lambobin yabo a gun gasannin wasannin Olympic ba. Amma Mr. Munshi ya ce, "Ruhun gasar wasannin Olympics shi ne halartar wannan gasa, ko ka samu nasara ko ba za a iya samun nasara ba a gun gasar suna matsayi na biyu. Yanzu za a shirya wannan gasar wasannin Olympics a nan kasar Sin, tabbas ne za mu kara yin kokarinmu domin halartar wannan gasa. Kuma muna fatan za mu iya ciyar da wasannin motsa jiki na kasarmu gaba ta hanyar yin hadin guiwa da kasar Sin. A waje daya kuma, 'yan wasannin motsa jiki za su samu damar bayyana kansu ga masu sauraro."

Game da bikin kaddamar da gasar wasannin motsa jiki, Mr. Munshi ya ce, bikin kaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta musamman da aka yi a birnin Shanghai na kasar Sin a shekarar da ta gabata ya ba shi alama sosai. 'Yan wasannin motsa jiki da suka zo daga yankuna da kasashe kimanin 170 sun halarci wannan gasa. Kasar Bangladeshi ma ta aika da wata kungiyar da ke kunshe da 'yan wasannin motsa jiki kusan 40. A gun gasar, sun samu sakamako mai kyau. A gun irin wannan kasaitacciyar gasa, an iya shirya bikin kaddamar da ita da kyau, shirye-shiryen da aka nuna a gun bikin ma sun jawo hankulanmu sosai. Mr. Munshi ya ce ya yi mamaki kwarai. Sabo da haka, Mr. Munshi ya ce, yana cike da imani cewa, bikin kaddamar da gasar wasannin motsa jiki na Olympics ta Beijing zai samu nasara. Kasar Sin tana da dogon tarihi da wadatattun al'adu. Yana tsammani, ya kamata a nuna dukkan muhimman al'adun gargajiya na kasar Sin a cikin shirye-shiryen bikin kaddamar da gasar wasannin motsa jiki na Olympics ta Beijing. Mr. Munshi ya ce, "Mai yiyuwa ne ana ganin cewa wasu al'adu ba su da muhimmanci ga zaman rayauwar jama'a ta yanzu. Amma ina ganin cewa, kamar yadda sauran kasashen duniya suke yi, al'adun kasar Sin suna kuma samun cigaba a kai a kai, kowane mataki yana da halin musamman da muhimmancinsa. Ya kamata a yi kokarin harhada muhimman al'amuran tarihi na kasar Sin, musamman muhimman samakamon da jama'a suka samu a cikin tarihi a gun bikin kaddamar da gasar sabo da su ne suka kirkira tarihinmu."

Mr. Munshi ya kara da cewa, jama'ar kasar Bangladeshi suna farin ciki kwarai, kuma suna jin alfahari domin za a shirya gasar wasannin Olympics a kasar Sin. A idon jama'ar kasar Bangladeshi, kasar Sin tana kasancewa kamar wanta yaya ga dukkan kasashe masu tasowa. Idan kasar Sin za ta iya samun nasarar shirya wannan gasar wasannin Olympics, wannan ba abin alfahari ne na kasar Sin ba, jama'ar kasar Bangladeshi ma za su ji alfahari. Bugu da kari kuma, Mr. Munshi yana fatan za a yada tunanin "dukkan mutanen da suke da zama a yankuna daban daban na duniya 'yan uwa ne" da na "kafa wata duniyar da ke cike da jituwa" a duk fadin duniya. Mr. Munshi ya ce, "Kasar Bangladeshi abokiya ce ta kasar Sin. Jama'ar kasar Bangladeshi 'yan uwa ne na Sinawa. Ina fatan kasashen biyu za su kara yin hadin guiwa a fannoni daban daban, kuma irin wannan hadin guiwa za ta kawo moriya ga bangarorin biyu. Kamar kirarin gasar wasannin Olympics ta Beijing shi ne 'duniya daya, mafarki daya'. Sinawa suna da mafarkinsu, jama'ar Bangladeshi ma suna da mafarkinsu. Ya kamata dukkanmu mu yi kokari tare wajen kyautata zaman rayuwarmu kamar yadda 'yan uwa da abokai suke yi tare."

Da karshe dai, cikin harshen Sinanci ne jakada Munshi ya bayyana fatan alherinsa ga gasar wasannin Olympics ta Beijing. "Ina murnar gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta samu nasara. Ina fatan kowa yana lafiya, kuma zai samu arziki. Na gode muku kwarai da gaske."

To, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau na "Gasar Olympics ta Beijing a idon jakadun kasashen duniya da ke nan kasar Sin" daga nan sashen Hausa na CRI. Sanusi ya shirya muku wannan shiri kuma ke cewa a kasance lafiya.(Sanusi Chen)