Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-25 16:59:33    
Beijing ya cika alkawarinsa na shirya wata gasar wasannin Olympic da ke da muhalli mai inganci

cri

A ran 25 ga wata, mataimakiyar shugaba, kuma kakakin ofishin kwamitin kawatar da muhallin birnin Beijing madam Wang Sumei ta ce, yawan fadin bishiyoyi da ciyayi da aka dasa a birnin Beijing ya kai kashi 43 cikin kashi dari bisa jimlar fadin birnin yanzu daga kashi 36 cikin kashi dari a shekara ta 2000. Sakamakon haka, birnin Beijing ya cika alkawarin da ya dauka a lokacin da yake neman izinin shirya gasar wasannin Olympic, wato ya zuwa lokacin yin gasar wasannin Olympic a karo na 29, ya kamata yawan fadin wuraren da aka dasa bishiyoyi da itatuwa ya kai kashi 40 cikin kashi dari.

A gun wani taron manema labaru da aka yi a cibiyar yada labaru ta kasa da kasa a nan birnin Beijing, madam Wang Sumei ta bayyana cewa, lokacin da ake kawatar da muhallin Beijng, an sanya dan Adam a gaban kome, kuma an yi ta dasa bishiyoyi da ciyayi a sabbin wurare tare da kyautata tsoffin wuraren da ke da bishiyoyi da ciyayi. Sakamakon haka, matsakaicin yawan fadin wuraren da ke da bishiyoyi da ciyayi ya kai murabba'in mita 12.6 yanzu daga murabba'in mita 9.66 a shekara ta 2000.

Bugu da kari kuma, tun daga shekara ta 2000, birnin Beijing ya gina manyan masana'antu 9 domin tsabtace ruwa maras tsabta. Sabo da haka, yawan ruwa maras tsabta da aka sarrafa shi ya kai kashi 92 cikin kashi dari bisa na dukkan ruwa maras tsabta da ake fitarwa a birnin Beijing. A waje daya kuma, birnin Beijing ya samu sakamako mai kyau wajen yin tsimin ruwa da yin amfani da ruwan da aka tsabtace shi. (Sanusi Chen)