Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-25 16:34:19    
'Yan wasan Mexico suna himmantuwa wajen samun horo domin halartar gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Aminai 'yan Afrika, gasar wasannin Olympics ta Beijing na karatowa. Ko kusa sane da cewa, 'yan wasan kasar Mexico su ma suna himmantuwa wajen samun horo domin halartar gasar wasannin. Kwanan baya bada dadewa ba, kungiyar wasan tsunduma cikin ruwa ta Mexico ta gudanar da wata gasar nuna kwarewa ta tsunduma cikin ruwa a birnin Mexico, babban birnin kasar, inda mazauna birnin kimanin 5,000 suka kallaci gasar domin sa kaimi ga 'yan wasan kasar.

Ga wata yarinya sanye da tufan iyo mai launin shudi ta yi tsalle daga kan dandamali dake da nisan mita 10 daga doron kasa, sa'anan ta tsunduma cikin ruwa, inda ta nuna kwarewa a fannin wasan har ta burge masu kallo na kasar. Wannan yarinya 'yar wasa, sunanta Paola Espinosa, ana kiranta " Gimbiyar wasan tsunduma cikin ruwa a Mexico", wadda kuma jama'ar kasar suke kyautata zaton ita ce ta fi samun yiwuwar kwashe lambar yabo a gun gasar wasannin Olympics da za a gudanar a birnin Beijing na kasar Sin. A lokacin da wakiliyarmu ta kai mata ziyara don jin ta bakinta kan burinta a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing, ta furta cewa: " Har kullum nakan nuna himma da kwazo wajen samun kyakkyawan horo domin share fagen halartar gasar wasannin Olympics ta Beijing, wadda za ta kasance wata gasa ce gagaruma. Na san cewa, 'yan wasan tsunduma cikin ruwa na kasar Sin na da babban karfi a fannin wasan. Amma duk da haka, ina cike da imani tare da amincewa da mai koyar da ni. Ko da cikin mafarkin da nakan yi ma, ina kishin samun wata lambar zinariya a gun gasar wasannin Olympics".

Sunan mai koyar da 'yar wasa Paola shi ne Ma Jin daga kasar Sin, wadda kuma yanzu take yin aikin koyarwa har na tsawon shekaru biyar a kasar ta Mexico. Ita Ma Jin ta rigaya ta horar da wassu fitattun 'yan wasan tsunduma cikin ruwa. A 'yan shekarun baya, takan ja ragamar tawagar 'yan wasan Mexico zuwa wurare daban-daban na duniya don halartar gasanni iri daban-daban na wasan tsunduma cikin ruwa, wadanda suka samu lambobin yabo da dama. Madam Ma Jin tana mai cewa: " Ina ganin cewa, wani abu mafi muhimmanci a gare ni, shi ne 'yan wasa su amince da ni bayan na koyar musu fasahohi a fannin wasan tsunduma cikin ruwa. Ina farin ciki matuka da ganin cewa 'yan wasan suna himmantuwa wajen samun horo daga wajena".

Madam Ma Jin ta gamsu da samun wani saurayi mai suna Rommel Pacheco dake da shekaru 21 da haihuwa, wanda kuma yake samun horon wasan tsunduma cikin ruwa har na tsawon shekaru 13. Wannan dan wasa ya samu ci gaban a-zo-a-gani bayan da ya samu horo daga Madam Ma. Yana mai cewa: " Shekaru biyar ke nan da Malama Ma ta soma horar da ni a watan Mayu na shekarar 2003. Lallai na yi alfaharin samun wannan malama, wadda take yin aiki tukuru".

Jama'a masu sauraro, ko kuna sane da cewa, kasar Mexico tana da babban karfi a fannin wasan motsa jiki a yankin Latin-Amurka. Jagoran tawagar wasannin Olympics ta Mexico Mr. Carlos Padia ya fadi cewa: " Kasar Mexico na shirin aike da 'yan wasa da yawansu ya kai kimanin 150 da za su halarci gasannin wasan kwallon kafa da kuma wasan kwallon gora da dai sauransu".

' Yar wasa Paola ta taba zuwa nan Beijing domin halartar gasar wasan tsunduma cikin ruwa da kuma samun horo. Ta ce, tana begen sake zuwan nan. Tana mai cewa: ' Lallai ginin cibiyar wasan ninkaya wato Water Cube tana da girma da kuma kyan gani. Na hakkake, kasar Sin za ta iya gudanar da gasar wasannin Olympics dake cike da kauna". ( Sani Wang)