Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Yakubu Mohammed Rigasa, mai sauraronmu da ya fito daga jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ya aiko mana, malam Yakubu ya ce, ina so ku bani tarihi da kuma dalilin da yasa ake zagayawa da fitilar nan ta Olympic a kasashe daban-daban a duk lokacin da za a gudanar da gasar wasannin na Olympics.
A kan kunna wutar wasannin Olympics wasu watanni kafin an fara wasannin Olympics, sa'an nan, kamar yadda Yakubu ya ce, a kan yawo da fitilar a kasashe daban daban har zuwa lokacin fara wasannin Olympics. To, amma ina tarihi da kuma dalilin da ya sa ake wannan biki?
Masu sauraro, sanin kowa ne wuta na taka muhimmiyar rawa a zaman rayuwar 'yan Adam, kuma sarrafa wuta wani muhimmin ci gaba ne da adan Adam ya samu a tarihi. A zamanin da, al'ummomi da yawa na duniya sun nuna ladabi da biyayya ga wuta, kuma haka aka yi a kasar Girika ta gargajiya, ana ganin wuta abu ne mai tsarki. Sabo da haka, a kan sami wuta a muhimman bukukuwa, har ma a gun wasanni. A zamanin gargajiya, a lokacin da za a fara wasannin Olympics, a kan zabi 'yan wasa uku, don su rike wutar yola su gudu zuwa birane daban daban na fuk fadin Girika, su sanar da jama'a za a fara wasannin Olympics, kuma tilas ne su dakatar da fada. A lokacin, wutar ta kasance tamkar umurni ne na sosai, kome kazamin fada ake yi, tilas ne a dakatar idan an ga wutar. Lokacin da aka dawo da wutar zuwa garin Olympia kuma, za a soma wasannin Olympics. To, wannan shi ne asalin wutar wasannin Olympics.
Wutar wasannin Olympics babbar alama ce ta manufar wasannin Olympics, wadda ke alamar fata da mafarki, haske da walwala, zumunci da zaman lafiya da kuma zaman daidaici. A kan kunna wutar wasannin Olympics ne a gaban fadar Hera da ke garin Olympia, wato asalin wurin da aka fara yin wasannin Olympics. Sa'an nan, a kan bi hanyar gargajiyar Girika wajen kunna wutar, wato da farko, babbar fada a wurin ibada za ta karanta kasidu domin Appolo a gaban fadar Hera, sa'an nan, babbar fada za ta kunna wutar bisa wani madubin da ake kira Skaphia, wannan kuma hanya ce kadai da za a bi wajen kunna wutar wasannin Olympics. Sa'an nan, babbar fada za ta sanya wutar a cikin wani kwano, kuma da wutar ne za ta kunna fitilar da ke hannun mai yawo da wutar. Daga nan kuma, aka fara yawo da fitilar wasannin Olympics.
Masu yawo da wasannin Olympics mazanni ne da ke yada manufar wasannin Olympics. Kullum hukumar kula da wasannin Olympics ta duniya na ba da shawarar cewa, kamata ya yi jama'a su kasance masu fitilar wasannin Olympics, wato jama'a duk wanda ke iya rike da torcilan tare da kammala gudu cikin zangon da aka kayyade, to, yana da damar zama mai mika wutar yola ta wasannin Olympics.
Akwai ka'idoji da dama game da mika wutar yola, kuma muhimman ka'idoji sun hada da "wuta daya, hanya daya da kuma biki daya", wato wutar da ake yawo da ita tilas ne ta kasance wutar da aka samo daga garin Olympia, kuma ba za a iya hada wutar da sauran wuta ba. sa'an nan, ana iya gudanar da bikin yawo da fitilar wasannin Olympics daya kawai. An dai cimma wadannan ka'idojin ne bisa yarjejeniyar da hukumar kula da wasannin Olympics ta duniya da gwamnatin Girika suka kulla, har ma ka'idojin sun zama al'adu wajen mika wutar yola ta wasannin Olympics.
Bayan da aka kammala zagaya da fitilar wasannin Olympics a kasashe daban daban, daga karshe dai, za a kai fitilar zuwa babban filin wasannin Olympics da ke kasar da ta karbi bakuncin wasannin, kuma a kunna wuta a filin, to, an fara wasannin Olympics ke nan.
Masu sauraro, an dai kunna wutar wasannin Olympics na Beijing a ran 24 ga watan Maris na wannan shekara, kuma sa'an nan, an zagaya da wutar a birane 19 da ke waje, a yayin da yanzu ake ci gaba da zagayawa da wutar a birane daban daban na kasar Sin. Yau kwana fiye da 10 ne kawai ya rage a fara wasannin Olympics a nan birnin Beijing, kuma an riga an share fagen wasannin sosai da sosai. To, bari mu sa rai ga ranar da za a kai wutar zuwa babban filin wasannin Olympics a ranar 8 ga wata mai zuwa, mu sa rai ga wannan kasaitaccen biki na duk duniya.(Lubabatu)
|