Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-25 12:23:57    
Kungiyar wasan Tackwondo ta Nigaria na da aniyar kwashe lambobin zinariya a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Aminai 'yan Afrika, lallai kun san cewa, akwai 'yan wasa biyu na kungiyar wasan Tackwondo ta Nigeria da ba ta yi suna ba a duniya da suka samu izinin shiga irin wannan wasa a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing. Sanin kowa ne wasan Tackwondo ya samu asali daga kasar Korea ta Kudu, wanda kuma ba a fadada shi zuwa dukkan fadin nahiyar Afrika ba tukuna. Amma, kungiyar wasan Tackwondo ta Nigeria ta lashi takobin samun lambobin zinariya a gun gasar. To, yanzu bari mu dan gutsura muku wani bayani da wakilinmu ya ruwaito mana daga Nigeria.

Abun da ya wuce tsammanin wakilinmu shi ne ya bakunci kungiyar wasan Tackwondo ta Nigeria ne a gaban kofar ofishin jakadancin Jamus dake Nigeria, inda ya ga kyaftin kungiyar ta Nigeria da mai koyar da 'yan wasa da kuma 'yan wasa biyu suna cikin layi domin samun fasfot zuwa kasar Jamus. A can ne za su hadu da sauran 'yan wasan kungiyar kafin su zo nan Beijing don halartar gasar wasannin Olympics. Wakilinmu ya tambayi babban mai koyar da 'yan wasan Tackwondo na maza na Nigeria, Osita Egwu a kan cewa mene ne makasudin kungiyar ta Nigeria ? Mr. Egwu ya amsa cewa : ' Babban burinmu shi ne samun lambobin zinariya. A yanzu haka dai, mun rigaya mun kammala dukkan ayyukan share fage ga halartar gasar. Kamar yadda Hausawa sukan fadi cewa: Haka ta Cimma Ruwa."

Ban da wannan kuma, kyaftin kungiyar Nigeria Mr.George Ashiru yana mai cike da kyakkyawan fatan 'yan wasan za su sami maki mai kyau domin su ne 'yan wasa mafi nagarta a duniya a fannin irin wannan wasa na Tackwondo. Ya furta cewa: " Akwai 'yan wasa biyu daga cikin kungiyarmu da suka samu izinin shiga ayyukan wasa iri biyu na Tackwondo a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing. Ban da wannan kuma, wani dan wasa na kasarmu ya taba samun lambar azurfa ta wannan wasa na matakin jiki mai nauyi a gun gasar wasannin Olympics ta Barcerona a shekarar 1992. Kazalika, ana ganin cewa, 'yan wasa a matakin jiki mai nauyi mafi nagarta a duniya dukkansu na nahiyar Afrika ne. Kuma kungiyar Nigeria ta kasance mafi kyau a nahiyar Afrika. Saboda haka ne, zai yiwu mu samu lambobin zinariya".

Jama'a masu sauraro, wassu mutane na shakkar cewa shin ko ana iya horar da nagartattun 'yan wasan Tackwondo har da zakarun wasannin Olympics a Afrika? Game da wannan dai, Mr. Ashiru ya furta cewa, halin musamman na karfin jikin 'yan wasa na Afrika ya dace da 'yan wasan kwarai da gaske wajen yin wannan wasa mai ban sha'awa. Daga baya, Mr. Ashiru ya fadi cewa: "Cikin watanni 6 da suka gabata, mun sanya kokari matuka wajen samun horo tare da 'yan wasa na yankunan Arewacin Amurka, da Turai da kuma na Asiya".

Wani dan wasa Bahaushe daga arewacin Nigeria, Adamu Issah ya fada wa wakilinmu cewa: "Mun samu horo na tsawon watanni 3 a yankin Taiwan, inda na samu damar karawa da 'yan wasa na Asiya. Hakan ya inganta karfin da muke da shi na yin gasa".

Ana sa ran 'yan wasan Tackwondo na Nigeria za su ba wa 'yan-uwansu dake can nesa ba kusa ba na nahiyar Afrika mamaki daga nan Beijing. ( Sani Wang )