Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-25 16:38:27    
Beijing ya bude kauyuka biyu na manema labaru na wasannin Olympics

cri

Ran 25 ga wata da safe, an bude kauyuka biyu na wasannin Olympics na Beijing, an fara karbar manema labaru masu rajista kusan dubu 7 daga kasashe dabam daban na duniya.

A lokacin ake yin wasannin Olympics, kwamitin shirya wasannin Olympics ya shirya kauyuka biyu ga manema labaru masu rajista, wato kauyen manema labaru kirar "Green Homeland" da ke kusa da wurin shakatawa na daji na Olympics da kauyen manema labaru kirar "Huiyuan" da ke kusa da babbar filin wasa wasannin Olympics na Beijing kirar "Shekar Tsuntsu". A cikinsu, kauyen "Green Homeland" shi ne kauyen manema labaru mafi girma a tarihin wasannin Olympics.

A gun bikin bude kauyuka, manema labaru da yawa daga kasashen Sin, da Amurka, da Amurka, da Faransa, da Australiya sun zama baki na zagaye na farko wadanda suka fara zama a kauyuka. Madam Zhao Jinfang direkatar kungiyar gudanar da harkokin kauyukan manema labaru ta yi maraba da musu.

Yawan manema labaru masu rajista na wasannin Olympics na Beijing ya kai fiye da dubu 20. ban da kauyuka biyu, hotel fiye da 50 na birnin Beijing za su karbi musu.