Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-24 18:05:10    
Birnin Beijing yana kokarin tabbatar da zirga-zirga domin gasar wasannin Olympic

cri

Haka kuma, a lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing, dubban 'yan kallon gasar na ketare za su zo birnin Beijing. Sabo da haka, hukumar zirga-zirga ta Beijing ta tsai da kudurin cewa, 'yan kallo za su iya daukar wasu kayayyakin ababen hawa, ciki har da jiragen kasa da ke tafiya a karkashin kasa tare da tikitinsu. Bugu da kari kuma, za a kebe hanyoyin kayayyakin ababen hawa 34 da suke zuwa dakuna da filayen gasar wasannin Olympic a lokacin gasar. Mr. Liu Xiaoming, shugaban kwamitin sa ido kan babbar zirga-zirgar jama'a na Beijing ya ce, "Bisa ajandar gasar, ba ma kawai mun daidaita kuma da kyautata hanyoyi da lokaci na babbar zirga-zirgar jama'a ba, mun kuma tsara hanyoyin kayayyakin ababen hawa 34 domin wannan gasa musamman. Za a kaddamar da wadannan hanyoyi ne bisa ajandar gasar a kai a kai domin ba da hidima ga 'yan kallo."

Bayan da aka soma aiwatar da manufofin tabbatar da zirga-zirgar gasar wasannin Olympic ta Beijing, yawancin mazauna Beijing za su dauki kayayyakin ababen hawa. Yarinya Long Xuanxun ta ce, "Ni wata daliba ce, na kan dauki kayan ababen hawa. Bayan da aka aiwatar da manufar kayyade yawan motoci bisa lambobinsu, a bayyane ne yawan motocin da ke tafiya a kan titi ya ragu sosai, kuma kusan babu cunkuso a kan hanya." (Sanusi Chen)


1 2