Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-24 15:18:15    
Manyan kamfanonin watsa labaru na kasa da kasa suna mai da hankula sosai kan gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Bisa kusantowar lokacin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing, manema labaru da yawa sun kara mai da hankulansu kan birnin Beijing. Manyan kamfanonin watsa labarai da yawa na kasa da kasa ciki har da Associated Press ta kasar Amurka, da Agence Farance-Press na kasar Faransa, da the Reuter Led. da dai sauransu sun riga sun shiga cikin babbar cibiyar watsa labari ta gasar wasannin Olympics ta Beijing, a cikin yakini ne, suna share fage domin cin nasarar yakin watsa labari game da gasar wasannin Olympics.

Ana kyautata zaton cewa, a yayin da ake shirya gasar wasannin Olympics, zai kasance da manema labarai da yawansu zai zarce dubu 20 da ke zauna a babbar cibiyar watsa labarai da cibiyar rediyon kasa da kasa domin bayar da labarai game da gagarumar gasar wasanin Olympics. Fadin babbar cibiyar watsa labarai ta gasar wasannin Olympics ta Beijing ya kai muraba'in mita dubu 6 da dari 3, wadda ta fi girma a duk tarihin Olympics.

Injiniya da ke kula da harkokin internet na Associated Press ta kasar Amurka wato Mr. Ben Bonnet ya gaya mana cewa,

'A halin yanzu dai, muna da masu fasahohi da yawansu ya kai 22 da ke aiki a babbar cibiyar watsa labarai. Muna kaddamar da cudanya da ke tsakaninmu da filaye da dakunan wasanni, musamman ma wadannan suke nesa da mu.'

Wani ma'aikacin the Reuter Led. mai suna Zhou Xuanlian ya gaya wa wakilinmu cewa, 'Dukkan ma'aikatan the Reuter Led. za su iso wannan wuri. Fiye da goma daga cikinsu za su gudanar da harkokin fasaha, manema labarai suna da yawa, har yawansu zai zarce dari.'

Manemin labaru na Agence Farance-Press na kasar Faransa Mr. Denis Achard ya ce, 'A halin yanzu dai, muna da mutane hudu ko biyar, muna kaddamar da na'urori ga wakilanmu na marubuta da na daukar hotuna. Wadannan manema labarai ba su hada da zaunannun wakilanmu a birnin Beijing kawai ba, har ma sun hada da ma'aikata da yawa da za a tura daga reshen kamfanonin watsa labarai daga kasa da kasa na Agence Farance-Press na kasar Faransa.'(Danladi)